Kwanan baya, gwamnatin kasar Canada ta gabatar da sabunta rahoton kudinta mai taken “sanarwar tattalin arziki a lokacin kaka”, inda ta yi shirin kara dora haraji kan wasu kayayyaki masu aiki da makamashin hasken rana da wasu ma’adanai da za su shigo daga kasar Sin a farkon shekarar badi. Ban da wannan kuma, rahoton ya bayyana shirin ware kudi dala miliyan 903 cikin shekaru 6 masu zuwa a bangaren kare tsaron iyakokinta.
Manazarta na ganin cewa, Canada na shirin daukar matakin kare tsaron iyakokinta da kara dorawa kasar Sin haraji ne don nuna biyayyarta ga Amurka, duba da cewa zababben shugaban Amurka Donald Trump ya taba yin barazanar kara dorawa kayayyakin da za a shigo da su daga Canada haraji da kashi 25%, da zarar ya hau kujerarsa.
- NDLEA Ta Kama Mutane 415, Ta Ƙwace Tan 1.2 Na Ƙwayoyi A Bauchi
- Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Dokar Haraji – Tinubu
Kazalika, daga baya, ya kara kawowa Canada barazana bisa hujjar tsaron iyaka da rashin samun dacewa tsakanin matakan da bangarorin biyu suka dauka kan haraji da suke son aiwatarwa a kan kasar Sin. Don haka gwamantin Justin Trudeau na kwadayin Amurka ta soke barazanar da Trump ya yi ta karawa Canada haraji bisa wadannan matakan da ya dauka.
Amma, matakan da Trudeau ya dauka za su tafi a banza, saboda Donald Trump dan kasuwa ne, tunaninsa na neman samun moriya mafi girma ba zai canja ba, baya ga haka yana mai da moriyar gwamnatinsa a gaban komai, ba zai yi la’akari da muradun kawayen kasarsa ba ko kadan.
Nuna biyayya ga Amurka don neman samun moriyar siyasa a gajeren lokaci, ba shakka ba wai zai illata huldar ciniki tsakanin Sin da Canada ne kawai ba, abin zai shafi hatta ‘yancinta na gudanar da harkokin kasa da kasa wanda zai bace sannu a hankali, kuma daga bisani za ta zama ’yar amshin shatan Amurka kurum! (Mai zane da rubutu: MINA)