A makon jiya ne Shugaban kungiyar Sufuri ta RTEAN, Ambasada Dakta Musa Maitakobi ya samu nasarar lashe zaben zama Ma’ajin kungiyar Kwadago ta TUC, wannan ba karamin nasara bace, wakilinmu Bello Hamza, ya tattauana na shi, inda ya tabo al’amura da dama da suka shafi harkokin kungiyar da yadda ya shirya bunkasata ta yadda za ta yi daidai da zamanin da muke ci, ya kuma yi bayanin halin da ake ciki a kan shirin samar da motoci masu amfani da iskar gas.
Ya bayyana cewa ‘’Zamu nemi filaye a wuraren da muka ga ya dace don gina wannan gidajen mai, Insha Allahu zamu gina. Bankin Kasa ya kira mu mun zauna dashi ya kuma ce mu kawo tsarin mu yadda Yakamata mu yi su gani, na biyu akwai kanfanoni masu zaman kansu da hadin guiwar representatibe na ministan cikin gida a bangaren man fetur suma ina tabbatar maka sun zo mun zauna da su mun yi bayanai na gamsuwa na inda ya dace da inda za’a gina wannan da kuma share da za a bayar.
- Yadda Hare-Haren ‘Yan Bindiga Suka Shafi Rayuwar Al’umma A Kagara – Rahoto
- Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju
Daga kan su membobi da kanfanoni da za su shigo wannan tafiya.
Ya kuma kara da cewa “A Yanzu na gaya na akwai kafanoni guda biyu, da wani dream energy, Wanda suna cikin wannan tafiya. Amma har zuwa yau maganar cewa bankin kasa ko Akwai wani kudi da ya ware don ya bamu don ayi wannan aiki, tukunna.
“Muna dai zama dasu suma hanyar da suke ganin zasu taimaka toh zasu taimakawa.
“Lokacin ma’ana abin da nake nufi a ban duk lokacin da suka fito suka gaya mana ga irin taimakon da zasu bamu, na kudi ne, na bashi ne da ruwa, ko ba ruwa, duk ba zan iya baka labari ba domin bamu gama zama dasu ba”.
Ya ce, za a samu hadin kai ne da wasu kungiyoyi don ya tabbatar da nasasar wannan shirin, a kan haka ya nemi hadin kai na dukkn masu ruwa da tsaki don tabbagytar da samun nasafrar wannan aikin da aka sa a gaba.