‘Yan bindiga sun tare wani magidanci a yankin Gidan Abe, Ƙaramar Hukumar Kachia, Jihar Kaduna, suka ƙwace kayan abincin Kirsimeti da ya saya, ciki har da buhun shinkafa da kayan miya.
Basaraken yankin ya tabbatar da cewa maharan, waɗanda suka zo kan babura, sun kai harin ne a ranar Asabar yayin da mutumin ke dawowa daga sayayyar kayan abincin a Katari.
- Sin Na Matukar Adawa Da Binciken Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Sana’o’in Na’urorin Lantarki Na Kasar Sin
- Ma’aikatar Kudin Sin Ta Lashi Takobin Kara Kashe Kudade A 2025
Ya ce maharan sun tsayar da mutumin da bindiga, suka kwace kayan abincin Kirsimetin sannan suka tsere, amma ba su sace mutumin ko kuma ji masa rauni ba.
“Na samu labarin cewa maharan sun tare mutumin a hanyarsa ta dawowa Gidan Abe daga Katari, inda suka ƙwace kayan abincinsa,” in ji basaraken.
Jin ta bakin kakakin ’yansandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, domin karin bayani ya ci tura.