A yau Litinin ne hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta fitar da rahoton farko kan ci gaba da aka samu wajen gudanar da bincike da aikace-aikace na kimiyya a tashar sararin samaniyar kasar, inda ta bayyana sakamako 34 tun bayan da aka kammala tashar a ranar 31 ga watan Disambar 2022.
Akwai sakamako 13 da suka danganci rayuwar sararin samaniya da binciken dan adam, 12 a ciki bincike ne na kimiyyar lissafin mafi kankantar nauyi wato microgravity, da kuma 9 a fannin sabbin fasahohin sararin samaniya da aikace-aikace binciken.
- Dr. Maryam Yola Ta Zama Farfesa Mace Ta Farko Kan Magungunan Gargajiya Da Al’adun Hausa
- Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta
Wadannan sakamakon gudunmawa ce daga kungiyoyin bincike na kimiyya 63 a duk fadin kasar, tare da fiye da 500 na manyan kundayen kimiyya da aka wallafa, gami da samun ikon mallakar fasahohi sama da 150.
Tashar za ta gudanar da ayyukan bincike sama da 1,000 a cikin shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa, tare da aiwatar da aikin yada kimiyya da hadin gwiwa a duniya, a cewar CMSA. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp