Gwamnatin jihar Kano ta sake fatali da kudirin sake fasalin dokar haraji gabanin majalisar dokokin kasar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya yi magana ta bakin Mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya nanata matsayar gwamnatin a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 da aka gudanar a filin wasa na Filin Mahaha, Kofar Naisa, a wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar.
- Wannan Jawabi Ya Karfafa Zuciyarmu a Fannoni Uku
- Sojin Ruwa Sun Yi Alƙawarin Ƙara Haƙo Gangar Mai Miliyan 3 A Kowace Rana
Gwamnan ya ce, “Wannan kudiri na sake fasalin dokar haraji ba shi ne mafita ga kalubalen tattalin arzikinmu ba. Jihar Kano ba ta goyon bayan duk wata manufar da za ta yi illa ga rayuwar al’ummarmu.”
Ya yaba da hakuri da juriyar da mazauna Kano suka nuna a cikin matsin tattalin tattalin arziki da ake fama da shi, inda ya bayyana shirin kara harajin a matsayin “wanda ya zo a kure, kuma yana da illa ga hadin kan kasa. ‘Yan Nijeriya gaba daya, musamman arewa na fama da kuncin rayuwa da rashin tsaro da ba a taba ganin irinsa ba, don haka ya kamata fadar shugaban kasa ta kara maida hankali wajen magance matsananciyar talauci da yunwa, musamman a yankin Arewacin kasar nan.”
Mataimakin gwamnan ya ja hankalin al’ummar Kano da su ci gaba da kasancewa da hadin kai da tsayin daka, inda ya ce, “Muna fata 2025 ta zama shekarar wadata da ci gaba, mu gina Jiharmu mai albarka tare”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp