Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 7 ga watan Satumba domin sauraron karar da ke neman a haramta wa Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC takara a zaben 2023.
Masu shigar da kara, jiga-jigan jam’iyyar APC guda hudu, sun nemi kotu ta yanke hukuncin cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba a matsayin dan takarar jam’iyyar saboda zargin ya mika takardun bogi na makarantun da ya yi ga hukumar zabe ta kasa (INEC).
- Sin Ta Kare Matakan Martani Da Ta Dauka Kan Yankin Taiwan Saboda Ziyarar Pelosi
- Kungiyar ASUU Ta Bukaci Soke Jarrabawar Jami’ar Jihar Kaduna
An dai zargi Tinubu da gabatar da takardun bogi lamarin da ya janyo cece-kuce da tarin muhawara mai zafi.
Hakazalika, an zarge shi da aikata laifuka da suka shafi harkokin safarar miyagun kwayoyi da kuma badakalar gidaje a kasar Amurka.
Sai daj dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC, ya dukkan zarge-zargen da ake masa.
Tinubu zai kara zaben shugaban kasa na 2023 da Atiku na jam’iyyar PDP, Peter Obi daga jam’iyyar LP sai kuma Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP.