• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Japan Ta Bai Wa Nijeriya Bashin Dala Miliyan 108 A Matsayin Daukin Gaggawa Don Samar Da Abinci

by Abubakar Abba
10 months ago
Japan

Kasar Japan, ta bai wa Nijeriya bashin dala miliyan 108 a matsayin daukin gaggaka don samar da abinci a kasar.

Jakadar Kasar Japan, Yuka Furutani da ke ofishin Jakadancin kasar a nan Nijeriya ce ta sanar da hakan; a wani taron bita da aka shirya wa wasu malaman aikin gona ta hanyar fasahar zamani, wadda aka gudanar a Abuja.

  • Ya Kamata Tuba Daga Laifin Yaki Da Tsoffin Sojojin Japan Ke Yi Ya Zama Matsaya Guda Ta Daukacin ‘Yan Siyasar Japan
  • Da Alamu Japan Ta Shirya Gyara Kuskurenta

Hukumar Aikin Noma ta Afirka da ke bayar da shawara a fannin aikin noma (AFAAS), tare da hadin gwiwar Kungiyar Aikin Noma ta Afirka Sasakawa da Cibiyar Aikin Noma ta Kimiyya (AGRA), da kamfanin tuntuba na Sahel da kuma shirin Aikin Noma na Afirka ne suka shirya taron a kwanakin baya.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce, ta dauki nauyin shirin; wanda aka gudanar a Jihohin Oyo, Gombe da kuma Kaduna.

A cewar Furutani, Gwamnatin Kasar Japan; na ci gaba da mayar da hankali wajen sama wa kasasehn Afirka da ke fama da karancin abinci bashi.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

Ta sanar da cewa, a watan Afirilun 2024; Nijeriya da Japan, sun rabbata hannun yarjejeniya a wani taro na kasa da kasa da aka gudanar a Tokyo kan yadda Japan za ta samar da bashin dala miliyan 108 ga Nijeriya.

Kazalika, ta bayyana cewa; Japan ta kara fadada wannan bashin zuwa akalla dala miliyan 4.2, domin kara habaka samar da Irin noman Shinkafa a Nijeriya.

A nasa jawabin, Daraktan Kungiyar Aikin Noma ta Afirka Sasakawa da ke Nijeriya, Godwin Atser wanda ke jagorantar aikin ya bayyana cewa; Gidauniyar Bill da Melinda Gates ce, ta zuba makudan kudade; don gudanar da aikin, wanda kuma za a  gudanar da bincike a Jihohin Oyo, Gombe da kuma Kaduna.

Godwin ya sanar da cewa, za a gudanar da binciken ne; domin gano adadi da kuma malaman aikin gona, musamman don lalubo mafitar da ake bukata ta bai wa kowane jinsi damar duba sauyin noma a Nijeriya, musamman a kan amfanin gona na Masara, Farin Wake, Rogo, Waken Suya da kuma a fannin dabbobi.

Muna da manhajar fasahar zamani iri-iri da aka samar da za iya amfani da su, don jawo manoma a jiki tare da ba su kariyar da ta dace”, in ji shi.

Godwin ya kuma yi nuni da cewa, idan aka kara habaka noma; hakan na nuna cewa, an tunkari turbar rage talauci a cikin al’umma, musamman duba da cewa; kashi 70 cikin 100 na a’lummar da ke zaune a karkara, sun dogara ne da fannin aikin noma.

Shi kuwa, Deola-Tayo Lordbanjou; Darakta a Hukumar Kula Bunkasa Ayyukan Malaman Aikin Gona ta Tarayya ya sanar da cewa, bisa wani bincike da aka gudanar, an gano cewa; akwai karancin ilimantarwa a fannin aikin noma a Nijeriya.

Deola-Tayo ya kara da cewa, malaman aikin gona sun fi yawa a shekarar 1980 a kasar, idan aka kwatanta da wadanda ake da su yanzu a fadin wannan kasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Babban jami’in JKS Ya Yi Kira Da A Nazarci Kuma A Aiwatar Da Tunanin Xi Jinping Kan Al’adu

Babban jami’in JKS Ya Yi Kira Da A Nazarci Kuma A Aiwatar Da Tunanin Xi Jinping Kan Al’adu

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.