Hukumar EFCC ta kori ma’aikata 27 daga aiki kan tuhumar zamba da aikata laifukan rashin ɗa’a a 2024. Hukuncin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin ladabtarwa na hukumar da Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya amince da shi.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce Olukoyede ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci cin hanci ba, kuma duk wani ma’aikaci da ake zargi za a bincike shi. Ya kuma yi bayani kan wani zargi da ake yi na dala $400,000 da wani ma’aikaci da ba a bayyana sunansa ba ya ce ya yi wa wani shugaban sashi.
- EFCC, ICPC Sun Kwato Naira Biliyan 277.69 Da Dala Miliyan 106 A Shekara Guda
- Daga Karshe, Yahaya Bello Ya Fada Hannun EFCC
Bugu da ƙari, hukumar ta gargadi jama’a kan ayyukan ɓata gari da ke amfani da sunan shugaban hukumar don damfarar waɗanda ake bincika. Haka kuma, an gurfanar da wasu mutum biyu, Ojobo Joshua da Aliyu Hashim, gaban kotu kan zargin neman dala miliyan ɗaya daga tsohon Shugaban NPA, Mohammed Bello-Kaka, don “sauƙaƙa wa” kan bincike da ba a yi ba.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su kai rahoton irin waɗannan bata gari, tana mai cewa Shugaban EFCC mutum ne mai mutunci wanda ba zai yi sakaci da gaskiyarsa ba.