Gwamnan jihar Ribas kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike ya lashi takobin cewa al’ummar jihar ba za su zabi duk wani dan takarar da bai ganin darajar jihar.
Ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da aikin babbar gadar sama ta Orochiri-Worukwo.
- Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Cafke Wadanda Suka Kai Hari Cocin Owo
- Dan Sanda Ya Mutu A Harin Da ISWAP Ta Kai Hanyar Maiduguri-Damaturu
Wike ya ci gaba da cewa, idan ka ce jihar Ribas ba komai na ce idan har ba su kaunar to mu ba ma kaunarsu.
Ya ce, babu wanda zai yi amfani da kuri’arsa a jihar domin kuri’unmu na da matukar mahimmaci.
Ya yi nuni da cewa a yanzu a harkar siyasa, ba wai kawai ka zabi dan takara ba ne, amma magana ce me za ka yi al’ummar jihar Ribas
An ruwaito cewa, furucin na Wike na zuwa ne dai dai lokacin da PDP a jihar Ribas ke fuskantar rikicin cikin gida da kuma a cikin jam’iyyar ta kasa.
In za a iya tunawa Wike da magoya bayansa da kuma magoya bayan dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar sun yi sabanin ra’ayi kan dauko Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin Atiku.