Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya amince da wasu sauye-sauye a majalisar zartarwa jihar, da niyar ruvanya kokarin gwamnatin na ajandarsa ta gina gobanka.
Sauye-sauyen sun hada nada sabon Kwamishina, Alhaji Malik Anas a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta Jihar Katsina.
- Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Shirin Ci Gaban Al’umma
- Gwamna Radda Ya Rufe Makarantun Da Ba Su Da Rajista A Katsina
Alhaji Anas dai yana da digiri na biyu a fannin sha’anin mulki da kasuwanci wanda ya yi karatunsa a jami’ar Bayero da ke Kano, sannan ya rike mukamai da suka hada da babban akanta janar na Jihar Katsina da mai ba da shawara kan harkokin kudi da banki
Haka Kuma an sauya wa Alhaji Bello Hussaini Kagara, wanda ya rike kwamishina a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare, inda yanzu aka mayar da shi ma’aikatan kudi ta jihar a matsayin kwamishina.
Hon. Bashir Taminu Gambo wanda ya rike mukamin kwamishinan ma’aikatan kudi yanzu an maida shi ma’aikatan kananan hukumomi da masarautu ta Jihar Katsina a matsayin kwamishina.
Kazalika, an samu wasu sauye-sauye a ma’aikatar ayyuka na musamman, inda Hon. Yusuf Rabi’u Jirdede yake kwamishinan wanda yanzu kuma an maida shi ma’aikatan ciniki da zuba jari ta Jihar Katsina.
Sai kuma Hon. Adnan Nahabu wanda yake a ma’aikatar ciniki da zuba jari, yanzu kuma an maida shi ma’aikatar ayyuka na musamman ta Jihar Katsina.Â
Gwamna Radda ya umarci sabon kwamishinan da kuma wadanda aka sauyawa wuraren aiki da su kasance sun yi aiki mai nagarta.Â
Gwamnan Katsina ya yi kira ga kwamishinan harkokin kudi da tsare-tsare da ya tabbatar ya yi aiki da manufofin gwamnatin mai ajanda gina gobanka tare da yin kiran sauran kwamishinonin da su ruvanya kokarinsu wajen ciyar da al’ummar Jihar Katsina.