Wani mummunan lamari ya faru a garin Gargajiga, ƙaramar hukumar Minjibir ta jihar Kano, inda ruftawar wata rijiya ta yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya, tare da jikkatar wasu biyu.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar. Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na safiyar Alhamis, 9 ga watan Janairu, 2025, yayin da wasu mutane uku ke aikin gyaran rijiyar.
- Wani Dattijo Ya Mutu Bayan Ya Faɗ Rijiya A Kano
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
Sanarwar ta bayyana cewa bangon rijiyar ya rushe, inda ya binne mutum ɗaya ƙasa kuma ya ja wasu biyu da ke bakin rijiyar. Ƙungiyar agaji daga shalƙwatar hukumar ta isa wurin misalin ƙarfe 12:20 na rana, inda aka ceto mutum biyu rai a hannunsu, yayin da wani mai suna Yusuf Nadabo, mai kimanin shekara 50, aka ciro shi cikin rashin numfashi kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
Dukkan waɗanda abin ya shafa an mika su ga dagacin garin Gargajiga, in ji sanarwar.