Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, CGI Isah Jere Idris ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya masu neman fasfo su tabbatar da cewa sun yi amfani da shafin intanet na hukumar wajen neman fasfo da biyan kuɗi ta nan, ga duk wani fasfo da suke so.
Ya yi kiran ne a Fatakwal a yayin ƙaddamar da Babbar Cibiyar Samar da Ingantaccen Fasfo Ta Zamani domin kawar da fasfo na tsohon ya yi a yankin kudu-maso-kudu. Ya bayyana cewa hukumar ta mayar da matakan neman fasfon zuwa shafin intanet ne domin daƙile duk wani nau’i na hada-hadar tsabar kuɗi a hannu wanda ta hakan ne ake ‘yan ƙumbiya-ƙumbiya. Don haka ya buƙaci masu neman fasfon su rungumi amfani da intanet, kana ya yi gargaɗin cewa mahukuntan hukumar za su hukunta duk wanda aka kama yana karɓar tsabar kuɗi a hannu a kan neman fasfo.
Sanarwar da mai Magana da yawun hukumar ta NIS, ACI Amos Okpu ya aike wa LEADERSHIP Hausa ta ƙara da cewa, shugaban hukumar ya yi ƙarin haske kamar haka; “Cibiyar Ingantaccen Fasfo da muke ƙaddamarwa a yau a nan, ɗaya ce daga cikin sauye-sauye da gyaran fuska da muke yi na ƙara inganta sha’anin fasfo ga ‘yan ƙasa. Bisa ƙaddamarwar ta yau, dukkan ofisoshin fasfo na Jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Kuros Riba da Ribas sun sauya daga masu bayar da tsohon fasfo zuwa sabo mafi inganci da aka samar,” in ji shi.
Bisa ƙaddamar da cibiyar dai, dukkan wani mai buƙatar fasfo a cikin waɗannan jihohin, ana sa rai ya cike takardar nema ta shafin intanet a direshin passport.immigration.gov.ng, tare da biyan kuɗi ta nan da kuma neman a ba shi ranar da zai zo a ɗauki bayanansa ta na’ura. Kuma ana buƙatar ya je ofishin fasfon ne kawai a ranar da aka sanya masa.
Tun da farko, Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ayyukan fasfo suna da matuƙar muhimmanci da ya kamata a ƙara mayar da hankali a kai sosai.
“Fasfo shi ne takarda ta shaidar ƙasa mafi muhimmanci da ya kamata ɗan ƙasa ya mallaka. Ba wai kawai yana bai wa mai shi damar tsallakawa zuwa ƙasashen waje ba ne, yana kuma nuna asalin ɗan ƙasa ne da ‘yancin da yake da shi. Saboda haka, ba wai kawai matakan samun fasfon ya kamata su zama sahihai bisa gaskiya da riƙon amana ba, ya dace waɗanda ke aikin samar da shi su kula sosai da yin abubuwa kamar yadda suka dace,” in ji shi.
Ministan ya yaba wa NIS bisa sauye-sauyen ci gaba da take aiwatarwa a sashen fasfo daga tsohon yayi da ake rubutawa da hannu zuwa na zamani da ake sarrafawa ta na’ura, a yanzu kuma zuwa ingantacce da ake yayi a duniya. Ya nunar da cewa ƙoƙarin da NIS take yi na ganin fasfon Nijeriya ya cika ƙa’idar inganci da Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) ta sharɗanta ba kawai abin yabawa ba ne amma gagarumin ci gaba ne abin alfahari.
Ya ƙara da cewa, sabon ingantaccen fasfon an samar da shi ne da fasahar zamani da ake ya yi a duniya wanda aka ƙawata shi da abubuwa na sirri guda 25 fiye da na wanda ake amfani da shi a yanzu. Sannan takardunsa suna da inganci ta yadda ruwa ba ya lalatawa kuma ‘yan damfara masu buga na jabu ba za su iya kwatanta irin sa ba.
Aregbesola ya sake nanata ƙudirin ma’aikatarsa ta ƙin amincewa da cuwa-cuwa da ka iya kawo tarnaƙi ga sauye-sauyen da ake yi inda ya yi gargaɗin cewa duk wani jami’i da aka kama da hannu a ciki zai fuskanci fushin doka. Ya yi kira ga masu neman fasfo su riƙa amfani da shafin intanet wurin gabatar da buƙatunsu tare da tabbatar da bayar da bayanai na gaskiya game da kawunansu domin komai ya tafi daidai-wa-daida.
A halin da ake ciki kuma, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike wanda mataimakiyarsa, Dakta Ipalibo Banigo ta wakilta a taron, ya yaba wa NIS bisa zaɓar Fatakwal a matsayin Babbar Cibiyar Samar da Fasfo ta yankin kudu-maso-kudu.
Ya ba da tabbacin cewa, jihar ta ƙudiri aniyar bayar da goyon baya ga dukkan hukumomin gwamnati da ke jihar, kana ya yi kiran ɗorewar sauye-sauye da garambawul da ake yi a kan batun fasfo domin ya inganta sosai.
Cikin manyan al’amuran da suka gudana a taron akwai ƙaddamar da cibiyar wacce za ta karaɗe jihohin kudu-maso-kudu da Ministan Cikin Gida Aregbesola ya yi bisa rakiyar mataimakiyar gwamnan Ribas.
Manyan jami’an gwamnati na jihar da na tarayya ciki har da wakilan sojoji da sauran hukumomin tsaro da ke jihar sun halarci taron.
Bisa ƙaddamar da katafariyar cibiyar fasfon dai, yankin kudu-maso-kudu ya bi sahun takwarorinsa na kudu-maso-yamma da wasu cibiyoyi da ke Amurka da Birtaniya wajen sauyawa daga bayar da fasfo na tsohon yayi zuwa sabo.