• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Abokin Daka Ake Shan Gari…

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Shaidu da abubuwa na zahiri na kara tabbatar da cewa, Sin da Afirka sun zama abin da Malam Bahaushe ke cewa, ’yan uwa rabin jiki”.

Duk lokacin da bangaren Sin ya ga abin da zai shafi moriyar kasashen Afirka da ma na kasashe masu tasowa, ya kan yi kokarin ankarar da duniya bukatar kare muradunsu tare da mara musu baya, wajen ganin an cimma burin da ake fata.

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Ra’ayin ‘Yan Afirka Kan Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka Ya Fi Muhimmanci

Batu na baya-bayan shi ne yadda zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, kuma shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya, da su goyi bayan Afirka wajen inganta karfinsu na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kasashensu. Zaman lafiya aka ce ya fi zama dan sarki, kuma sai da zaman lafiya, za a samu duk wani ci gaba da ake fata.

Zhang ya bayyana yayin taron bude muhawarar kwamitin sulhu da kasar Sin ta kira, mai taken “zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka: samar da karfin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.” Tallafin da kasar Sin din ta gabatar sun kasance a fannoni guda 4 ne, wadanda suka hada da karfafa sanin makamar aiki a fannin tafiyar da harkokin gwamnatoci, da inganta kwazon sassan hukumomin tsaro, da bunkasa ikon samar da ci gaba mai dorewa, da renon kwararru.

Jami’in na kasar Sin ya ce, bisa la’akari da irin kwarewar da kasar Sin ta samu wajen samun bunkasuwa, da gogewa daga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma darussan tarihi daga fadin duniya, kasar Sin ta yi imanin cewa, idan har ana son taimakawa Afirka wajen samun kwanciyar hankali na dogon lokaci, wajibi ne a kara zuba jari mai dorewa, da yin tunani mai zurfi, da kuma gina harsashi mai karfi ga Afirka, don kara karfin hanyar samun ci gaba da ta zaba da kanta, da inganta juriyarta kan abubuwan da za su kawo mata cikas daga waje. Sanin kowa ne cewa, sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Saboda muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ci gaban kowa ce kasa a fadin duniya, masu sharhi na kara jaddada cewa, bai kamata a rika gindaya wani sharadi na siyasa da ya shafi samar da taimako ba, kuma bai kamata a rika tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, ko maye gurbin ayyukan da kananan hukumomi suka saba gudanarwa.

Ba abu ne boyayye ba, baya ga kayayyakin more rayuwa da kasashen Afirka suka amfana da su karkashin hadin gwiwar sassan biyu, wato Sin da Afirka.

Daga lokaci zuwa lokaci ko dai a taruka ko dandalolin kasa da kasa, bangaren Sin kan yi kokarin kare muradun kasashe masu tasowa baki daya. Abin da ke kara tabbatar da sahihancin alakar sassan biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Next Post
Dole Ne A Hukunta Kasar Amurka Wadda Ta Fi Keta Hakkin Dan Adam A Duniya

Dole Ne A Hukunta Kasar Amurka Wadda Ta Fi Keta Hakkin Dan Adam A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.