Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, bisa ƙoƙarinsa wajen gudanarwa da yaɗa bayanai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
An yi masa wannan yabon ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai don kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa na shekarar 2025.
- Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates
- Karkashin BRI Sin Ta Yi Hadin Gwiwar Samar Da Dakunan Gwaje-gwaje Sama Da 70
Sanatocin sun jinjina wa ƙoƙarin ma’aikatar amma sun nuna damuwa kan ƙarancin kuɗaɗen da aka ware mata, suna masu cewa ba zai wadatar ba don aiwatar da aikin ta na yaɗa labarai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Sun buƙaci a samar da ƙarin kasafin kuɗi na musamman domin a ƙarfafa wa ma’aikatar gwiwa.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP-Kogi) ta jaddada bambancin kasafin kuɗin ma’aikatar da na ƙasar Afirka ta Kudu, inda ta bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Afirka ta Kudu ta samu kimanin naira biliyan 409 don aiwatar da shirye-shiryen ta.
Ta ce Nijeriya, wadda ke da yawan al’umma fiye da waccan ƙasar, ya kamata ta ware ƙarin kuɗi don shirye-shiryen ta na yaɗa labarai.
Ta kuma jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma, musamman matasa, da kuma yadda ministan da tawagar sa suke shirye don aiwatar da hakan idan aka ƙara masu kuɗi.
Shi kuwa Sanata Abdul Ningi (PDP-Bauchi) ya yaba wa ministan bisa ƙwarewar sa, jagorancin sa, da kuma cigaban da aka samu a hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, musamman ta fuskar cigaba da aka samu a Hukumar Tlabijin ta Nijeriya (NTA).
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Sanata Ken Eze (APC-Ebonyi), ya buƙaci ma’aikatar da ta ƙirƙiro hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
Ya kuma buƙaci a sake duba kasafin kuɗin, yana mai jaddada muhimmancin ɓangaren yaɗa labarai ga nasarar gwamnati.
Ya ce: “Ba za a iya yin abubuwa da yawa ba idan babu kuɗaɗen shiga, kuma bayanai suna da matuƙar muhimmanci: muna buƙatar ɓangaren ya jagoranci manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
“Kasafin kuɗin da ke gaban mu ba abin alfahari ba ne, idan an yi la’akari da abin da ake yi a wasu ƙasashe.
“Dole ne mu yi magana a matsayin ‘yan majalisa; dole ne mu ƙi amincewa da kasafin kuɗin ta hanyar kiran a ƙara yawan kasafin da aka ware wa ma’aikatar.
“Muna so Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa ya bayyana a gaban mu don sake duba kasafin kuɗin.”
A baya, ministan ya ƙiyasta cewa mafi ƙarancin adadin da ake buƙata don gudanar da ayyukan ma’aikatar yadda ya kamata ya kai naira biliyan 50.