Gwamantin tarayya ta zakulo kamfanonin jiragen sama guda hudu da za ta yi amfani da su wajen jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa kasar Saudiyya Arabiyya domin gudanar da aikin hajjin 2025.
Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai na kasa (NAHCON), Abdullahi Usman, shi ne ya shaida hakan ta cikin sanarwar da jami’ar watsa labarai na hukumar, Fatima Usara, ta fitar a ranar Lahadi.
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
Kamfanonin jiragen guda hudu da Nijeriya ta zaba a cewa sanarwar sun hada da Air Peace Limited, Fly-Nas, Mad Air, da kuma UMZA.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta shirya jerin matakan yin zabin a watan Nuwamban 2024 da nufin zabo nagartattu kuma wadanda suka dace, inda kamfanonin jiragen 11 suka cika bukatar neman a ba su damar yin jigilar.
Idan za a tuna dai hukumar ta kafa kwamitin mutum 32 da za su bi jerin kamfanonin jirage 11 da suka cika bukatar neman kwangilar jigilar da nufin yin zabin da ya kamata domin kyautata harkokin jigilar.
Mambobin da suka hadu a kwamitin tantance da zaben jiragen saman sun hada da wakilai daga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, mambobi uku daga hukumar kula da sararin samaniyan Nijeriya (NCAA) da kuma mamba guda daga hukumar kula da jiragen sama ta Nijeriya (FAAN), hukumar kula da lafiyar sararin samaniya (NAMA), hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET), da kuma hukumar NSIB.
Kazalika, an zabi mamba daya daga hukumar kwastam, da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC), an kuma dauki mambobi guda daga kowace shiyya a cikin mambobin majalisar NAHCON, shugabannin da suke kula da bangaren sufuri, Kasafi, harkokin shari’a, binciken kudi, ayyukan musamman dukka na NAHCON a matsayin mambobi a cikin kwamitin da kuma mamba daga masana’antar sufurin jirgin sama.
Bugu da kari, an zabi kamfanoni uku da za su yi jigilar kayayyaki yayin aikin hajjin da ke tafe. Wadanda suka samu tsallake tantance su ne, Aglow Abiation Support Serbices Limited, Cargozeal Technology Limited da kuma Kualla Inbestment Limited.