Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta gano motoci biyu da aka sace ta hanyar amfani da tsarin na’urar zamani (e-CMR), wanda aka samar don daƙile satar motoci a ƙasar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa ranar 1 ga Janairu, 2025, wasu mutane da ba a san su ba sun je wajen dillalin motoci a Zuba, Abuja, inda suka nuna sha’awa kan motar Toyota Corolla, samfurin 2014. A yayin gwajin mota, mutanen biyu suka nuna bindiga, suka tsoratar da dillalin, suka arce da motar tare da takardunta da mukullan mota biyu.
- Za A Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano Cikin Watanni 14 – Gwamnati
- SIMDA Ta Ƙulla Alaƙa Da Jami’ar Skyline Kan Ci Gaban Ilimi Da Kasuwancin Zamani A Kano
Haka nan, ranar 4 ga Janairu, 2025, an kai rahoton sace wata mota kirar Mercedes Benz C300 a gaban Luxirian Event Centre da ke Nassarawa GRA, Kano.
Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, CP Salman Garba, ya umarci jami’ai daga sashen yaƙi da satar motoci da su binciko motocin. A cewar SP Kiyawa, daga 10 zuwa 15 ga Janairu, 2025, jami’an sun yi amfani da bayanan e-CMR kuma suka gano motar Toyota a bayan tsohon Filin Jirgin Sama na Bauchi, yayin da aka gano Mercedes Benz a Shagari Quarters da ke Kano.
CP Garba ya yaba wa jami’an da suka gudanar da binciken tare da kira ga jama’a da su yi amfani da tsarin e-CMR wajen rajistar motocinsu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage satar motoci. Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin don tabbatar da doka da oda a jihar.