Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo zai bayar da shaida a yau a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) da ke birnin Paris kan shari’ar dala biliyan $2.3 da kamfanin Sunrise Power ya shigar da Nijeriya ƙara.
Kamfanin ya zargi gwamnatin da karya yarjejeniyar da aka ƙulla a 2003 don gina babbar tashar wutar lantarki ta Mambilla mai darajar dala biliyan shida a Jihar Taraba.
- Gwamnati Tarayya Ta Musanta Zargin Bai Wa Kamfanin Bogi Kwangilar Aikin Hanyar Abuja-Kano
- Gobara Ta Hallaka Mutum 66 A Otal Mai Hawa 12 A Turkiyya
Taƙaddamar ta fara ne bayan da kamfanin Sunrise Power ya ce gwamnatin ta saɓa yarjejeniyar da suka ƙulla.
Obasanjo ya musanta cewa ya amince da yarjejeniyar a lokacin mulkinsa, yana mai cewa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Olu Agunloye, ya yi aiki ba tare da izininsa ba.
A 2017, Sunrise Power ya shigar da ƙarar, inda ya nemi a biya shi diyya.
Duk da yarjejeniyar biyan dala miliyan 200 a wajen kotu da aka cimma a 2020, Sunrise daga baya ya nemi ƙarin diyyar dala miliyan 400, inda ya zargi gwamnati ta kasa cika alƙawari.
Lamarin shari’ar ya shafi wasu manyan mutane kamar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da Shugaban Sunrise Power, Leno Adesanya, wanda ya riga ya bayar da shaida a wannan mako.
Sakamakon shari’ar na iya yin tasiri sosai kan harkar wutar lantarki da kuma adadin diyyar da Nijeriya za ta biya.