A ƙoƙarinsa na kawo gyara ga yadda ake amfani da soshiyal midiya, musamman a tsakanin ‘yan siyasa da magoya bayansu, tsohon ɗan Majalisar Wakilai daga Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, Alhaji Hafizu Kawu, ya shirya wata bita ta musamman.
Taron, wanda aka shirya ƙarƙashin ‘Hafizu Kawu Media Team’ tare da haɗin gwiwar Majalisar Malamai ta Kano, ya mayar da hankali kan buƙatar tsaftace mu’amalar jama’a a kafafen sada zumunta.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
- Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Ƙudirori 15 Don Magance Yunwa
A cewar Hafizu Kawu, “Mun lura cewa yadda ake amfani da soshiyal midiya yanzu ya wuce inda ya kamata, musamman a siyasa.
“Wannan ya sa muka ga dacewar gayyatar malamai, waɗanda za su taimaka wajen wayar da kai game da muhimmancin zumunci da mutuntawa. Siyasa bai kamata ta zama hanyar raba kan al’umma ba.”
Dalilin Shirya Bitar
Da yake ƙarin bayani kan dalilin shirya bitar, Hafizu Kawu ya ce, “Bature ya ƙirƙiro soshiyal midiya ne domin sada zumunta da isar da saƙo cikin sauƙi.
“Amma mun ga yadda ake amfani da ita wajen yaɗa fitina da cin zarafi, wanda hakan ba daidai ba ne a addininmu.
“Wannan shi ya sa muka yi wannan taro domin ilmantarwa, domin magoya bayan jam’iyyu daban-daban su fahimci muhimmancin adawa mai tsafta da mutuntawa.”
Ya ƙara da cewa, “Mun gayyaci malamai kamar Sheikh Ibrahim Khalil, Dokta Aminu Daurawa, da Farfesa Abdallah Uba Adamu saboda su taimaka wajen faɗakarwa da ilmantar da jama’a.
“Malamai ne ke da tasiri wajen wayar da kan jama’a, kuma mun gode da irin gudunmawar da suke bayarwa.”
Ra’ayoyin Jama’a Kan Bitar
Game da martanin jama’a kan bitar, Hafizu Kawu ya bayyana cewa taron ya samu karɓuwa sosai.
Ya ce, “Mutane sun yaba da taron. Wasu ma sun ce da sun sani sun halarta, saboda ba a taɓa samun irin wannan ba a Kano.
“Mun samu damar haɗuwa da ‘yan siyasa daga ɓangarorin daban-daban tare da malamai domin tsaftace harkar soshiyal midiya.”
Kawu ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar faɗaɗa irin wannan bita nan gaba ta hanyar gayyatar jami’an tsaro da shugabanni da masu ruwa da tsaki.
Amfanin Taron Ga Jama’a
A cewar Hafizu Kawu, babban amfanin wannan taro shi ne ƙara fahimtar juna da kuma rage rigingimu a tsakanin ‘yan siyasa da magoya bayansu.
Ya ce, “Adawa halal ce, amma ta zama wajibi a yi ta cikin mutuntawa da gyara. Wannan zai taimaka wajen magance rigingimu, cin zarafi, da haddasa husuma.
“Kuma zai sa ‘yan siyasa su fahimci yadda za su yi amfani da soshiyal midiya don tallata manufofinsu ba tare da raba kan jama’a ba.”
Makomar Soshiyal Midiya a Siyasar Nijeriya
Hafizu Kawu ya ja hankalin shugabanni kan buƙatar wayar da kan matasa game da amfani da soshiyal midiya.
“Yanzu haka soshiyal midiya ita ce abin da ke karaɗe duniya. Dole ne mu ƙara dagewa wajen ilmantarwa da faɗakarwa domin kada mu tsinci kanmu a cikin wani hali da ba ma so.”
Ya kammala da cewa, “Dole ne gwamnatoci su bayar da goyon baya ga irin wannan hoɓɓasa, domin kare al’umma daga illolin amfani da soshiyal midiya ba tare da tsafta ba.”