An kammala wasan zagayen ƙarshe na rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai a wannan makon wanda yazo da abubuwa masu ban mamaki, wannan makon ya fitar da waɗanda za su kasance a zagaye na gaba, wadanda ke jiran tsammani da kuma ƙungiyoyin da aka kora suka dawo gida.
Manchester City ta zo daga baya ta doke Club Brugge da ci 3-1 wanda ya bata damar zamowa daga cikin masu jiran tsammani, yayin da Aston Villa da Arsenal suka iske Liverpool a zagaye na 16.
- Burkina Faso, Mali Da Nijar Sun Fice Daga ECOWAS A Hukumance
- Kofin Duniya: FIFA Ta Fitar Da Yadda Za A Samu Gurbin Zuwa Amurka
Celtic, wacce ta sha kashi a hannun Aston Villa da ci 4-2, ita ma za ta kasance a cikin wasannin share fage, yayin da dukkanin ƙungiyoyin Birtaniyya suka tsallake zuwa matakin gasar.
Waɗannan su ne ƙungiyoyin dake cikin kowane mataki:
Ƙungiyoyin Da Suka Kai Zagayen 16
Liverpool, Barcelona, Arsenal, Inter Milan, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Lille, Aston Villa.
Ƙungiyoyin Dake Jiran Tsammani
Atalanta, Borussia Dortmund, Real Madrid, Bayern Munich, AC Milan, PSV, Paris St-Germain, Benfica, Monaco, Brest, Feyenoord, Juventus, Celtic, Manchester City, Sporting, Club Brugge.
Ƙungiyoyin Da Aka Kora
Dinamo Zagreb, Stuttgart, Shakhtar Donetsk, Bologna, Sparta Prague, Leipzig, Girona, Red Star Belgrade, Sturm Graz, Salzburg, Slovan Bratislava, Young Boys.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp