Mahukunta a Masallacin Jami’ur Rahman, da aka fi sani da Masjid Sahaba a baya, sun dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar sallah da yin huɗuba, bayan wata huɗuba da ya yi a ranar 24 ga Janairu 2025 da ta jawo ce-ce-ku-ce a masallacin.
Sheikh Bin Uthman ya jagoranci tsohon masallacin Sahaba na tsawon shekaru 24 kafin gina sabon masallacin a kusa da shi wanda fitaccen ɗan kasuwar nan AY Maikifi ya gina. Wannan sabon wurin a baya filin shakatawa ne da jama’a ke taruwa don Sallar Juma’a da ta Eid.
- Bidiyon Dala: Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Da ‘Ƴansanda Da DSS Kan Kama Ganduje
- Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe Miliyan 95.4 Domin Gyara Masallatan Juma’a
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Malamin a huɗubarsa ta ranar Juma’a 24, ga Janairun 2025, Sheikh Bin Uthman ya bayyana yadda aka ware shi daga jagorantar sabon masallacin, duk da cewa shi ne tsohon limamin masallacin. Ya ce hukumar masallacin ta naɗa ƙarin limamai uku ba tare da yin la’akari da shi ba.
Bayan huɗubarsa, an samu wasu cikin mabiya masallacin sun fusata, har suka kusa kai wa sakataren kwamitin amintattun masallacin, Abdulƙadir Isawa, hari.
A wata wasiƙa da daraktan kula da masallacin ya sanya wa hannu, an sanar da dakatar da Sheikh Bin Uthman har sai an kammala bincike. An kuma buƙace shi da ya miƙa duka wata dukiyar masallacin da ke hannunsa.
A ranar Litinin, hukumar tsaro ta DSS da Majalisar Ulama sun kira Sheikh Bin Uthman da AY Maikifi don tattaunawa da su. A gefe guda kuma Majalisar Ulama ta shawarci Sheikh Bin Uthman da ya koma masallacinsa na asali, amma har yanzu dai ba a san ko zai amince da hakan ba.