Shugaban Kungiyar Masu Noman Inibi ta Kasa (GFAN), Abdullahi Dalhatu, ya bayyana Karamar Hukumar Kudan da ke Jihar Kaduna a matsayin wadda ke kan gaba wajen noman Inibi a fadin Nijeriya baki-daya.
Dalhatu, ya bayyana hakan ne a yayin da ya zagaya da Shugaban Karamar Hukumar ta Kudan, Dauda Iliya Abba; duba wata katafariyar gonar da aka shuka Inibi mai hekta biyar a yankin.
- Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.5bn A Auren Gata
- Gwamnatin Tarayya Da Kasar Faransa Sun Sake Sabunta Yarjeniyar Farfado Da Hakar Ma’adanai
Ya shaida wa Shugaban Karamar Hukumar ta Kudan cewa, a yankin ana yin noman Inibi da yawansa ya kai kimanin kashi 80 cikin 100.
A cewar tasa, a cikin watan Janairu kadai, an noma Inibi da yawansa ya kai akalla tan 22.
“A sashe daya na bishiyar ta Inibi, an girbe kimanin kilo 15 a shekarar farko da aka yi nomansa, inda kuma aka kara samun karin kilo 85 na Inibin da aka girbe.”
Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita.
“A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, Allah ya albarkaci Arewacin Nijeriya da kasar nomad a kuma yanayi mai kyau, musamman ma Karamar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, inda ake iya shuka wannan Iri na Inibi, ya girma; a kuma amfana da shi.
Shugaban ya sanar da cewa, kimanin kashi 85 cikin 100 na Inibin da ake nomawa a kasar nan, na fitowa ne daga Karamar Hukumar Kudan.
Shi kuwa, Shugaban Karamar Hukumar ta Kudan; Dauda Iliya Abba, yaba wa manoman ya yi, kan mayar da hankalin da suke yi a yayin noman nasu Inibi, inda kuma ya jaddada kudirin Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, na ci gaba da bai wa fannin aikin noma goyon bayan da ya dace.