Gwamnatin Jihar Katsina ta jaddada kudurinta na sayo karin kayayyakin hada Keke Napep masu amfani da wutar lantaki na kamfanin IRS ga masu haya domin saukaka harkokin sufuri a jihar.
Gwamna Radda ya ba da tabbacin hakan ne yayin gabatar da keke napep masu amfani da wutar lantaki guda dari biyar domin yin gwaji. Ya ce an sayo su ne da kudurin yin gwamji domin gane ingancinsu da kuma yanayin kula da su.
- Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
- Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.5bn A Auren Gata
Ya bukaci jagoran kungiyar tuka keke napep da ya zabi wasu amintattu su dubu biyar daga cikin mambobin kungiyar da za su ba da gudummuwarsu a cikin shirin.
Ya kara da cewa, gwamnatin na sa ran ganin sahihin rahoto kan amfanuwa da ‘yar kurkurar da ribar da aka samu da kuma jumurinsu.
Yayi nuni da cewa, wannan sabuwar fasahar za ta taimaka wajen rage yawan amfani da man fetur da kare muhalli daga gurbacewa da kuma rage hayaniyar ababen hawa.
Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar masu tuka ‘yar kurkurar, Jamilu Isyaku ya bayyana jin dadinsa ga Gwamna Radda bisa amsa kiran da suka yi masa na biya masu bukatunsu kan sama masu da keke napep mai amfani da lantarki da kuma ba da tabbacin yin amfani da su yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp