Bisa bayanan da aka samu daga wani dandali na shafin intanet, ya zuwa yau Talata, jimillar kudaden shiga da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a gidajen sinima a shekarar 2025 ta zarce kudin Sin yuan biliyan 11, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.5.
Bugu da kari, adadin masu kallo a lokacin bikin bazara na shekarar 2025 ya zarce miliyan 170, wanda ya karya tarihin baya na yawan masu kallo da aka taba samu lokacin bikin bazara, a tarihin fina-finan kasar Sin.
Har ila yau, bisa la’akari da yawan tikitin da aka sayar a shekarar 2025, yawan kallon fina-finan kasar Sin ya zarce na Arewacin Amurka, inda a halin yanzu ya zama na daya a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)