Assalamualaikum barkanmu da asubahin Asabar, takwas ga watan Muharram, shekarar 1444, bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da shida ga watan Agusta, shekarar 2022.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince a kashe wata Naira Biliyan 24, ga aikin noman rani domin bunkasa sana’ar noma.
- Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
- Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa
An tsaurara tsaro a gidajen yari da ke jihohin Kabbi, da Zamfara da Katsina, don dakile dukkan wani hari da za a iya kai wa gidajen.
Kungiyar gidajen rediyo da talabijin ta kasa BON, ta zargi hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin NBC, da yin azarbabi, da saba wa dokar NBC, da rashin adalci, a takardar tarar Naira Miliyan Biyar da ta kai wa gidan talabijin na Trust da wasu kafofin watsa labaru, a kan nuna wani bidiyo na rahoto a kan ‘yan ta’adda.
A jihar Kano ‘yan kwana-kwana sun yi nasarar sauko da wani matashi kasa, da ya makale a gada, ya ce ko Buhari ya sauka daga mulki, ko ya fado kasa daga gadar ya mutu.
A jihar Binuwai, gwamnan jihar Ortom, ya ce zai sayo wa ‘yan bijilanti na jihar bindigogi kirar AK47 don taimaka wa tsaro a jihar.
A Abuja an sace wani dan takaran gwamna na jihar Filato a jam’iyyar LP Yohanna Margif.
A jihar Sakkwato, da yake ‘yan makarantar da aka kashe Deborah za su koma makarantar ranar 8 ga watan nan wato jibi, gwamnatin jihar ta ce daliban za su biya kudi domin gyara kayayyakin da suka barnata.
A jihar Kaduna, ‘yan kungiyar Ansaru ne suke ta aure ‘yan matan yankin Birnin Gwari ana ta shagulgula.
Sai yankin Mando da ake ta korafi a kan badakalar da ake zargin an yi a rabon gidan sauro.
Sai kuma ma’aikatan hukumar yada labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an ba su ko taro na raba mutum da aikinsa rana tsaka ba, suna ci gaba da godon a biya su hakkokinsu.
A jihar Katsina, masu fashin jama’a da kisa da satar dabbobi ne, suke ci gaba da fashin matan aure da ‘yan mata, da kashe maza da tsofaffi.
LAHADI
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan wulakanci da Inyamurai suke ci gaba da yi wa Hausawa da ke zaune a kasashensu na Inyamurai.
Kungiyar dattawan Arewa ta yi tir da kisan wulakanci da Inyamurai suke ci gaba da yi wa Hausawa da ke zaune a kasashensu na Inyamurai.
Keyamo ya roki iyayen yara, su roki malaman jami’a su bude jami’o’i dalibai su koma aji.
Ya ce gwamnati ba za ta iya ciwo bashin Naira Tirilian 1.1 domin biyan bukatun malaman don kawo karshen yajin aikin da suke kai a yanzun haka ba, saboda ba ta da wannan kudi a yanzun. Kwalejin horar da kananan hafsoshin soja NDA, ta yi wa manhajarta gyara, tare da saitata domin ta iya tinkarar matsalar tsaro ta zamani da bullo wa matsalar ta bayan gida.
Kungiyar mamallaka gidajen rediyo da talabijin na AREWA, NBMOA a takaice, ta bukaci hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta kasa NBC a takaice, ta janye tarar Naira Miliyan Biyar da ta yi wa gidan talabijin na Tb Trust.
Yahaya Bello na jihar Kogi, ya tsaurara tsaro a jihar a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga, suka kashe Indiyawa biyu, da ‘yan sanda hudu a Ajakuta.
A jihar Taraba, masu fashin jama’a, sun kashe mutum uku, suka sace mutum ashirin da uku, suka korianoma daga gonakinsu.
A jihar Nasarawa, an kama wani akanta, da sitokifa, saboda bacewar takin zamani tirela tara.
A jihar Kaduna, dan takaran gwamna na jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isah Ashiru Kudan, yana yi wa al’umar musulmj na jihar Kaduna da duniya bakidaya, fatan alheri a wannan lokaci na azumin Ashura da Tasua da za a yi yau Lahadi da gobe Litinin, da addu’ar Allah Ya mana maganin matsalolin da kasar nan take ciki.
LITININ
Sojojin sama na Nijeriya sun ce sun yi nasarar gamawa da ‘yan ta’addan nan da suka kai wa ayarin shugaban kasa farmaki a hanyar ayarin ta zuwa Katsina don shirye-shiryen zuwan Buhari yin babbar Sallah da ya yi a Daura.
Kungiyar daliban Nijeriya ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwana bakwai ta sasanta da malaman jami’a, tare da bai wa shugaban kasa shawarar ya kori Adamu Adamu da Ngige.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta SERAP, ta kai gwamnatin tarayya kara kotu, a kan tarar Naira Miliyan Biyar da ta ci gidan talabjjin na TB trust da sauransu.
Shugabannin ‘yan Nijar mazauna Nijeriya, sun kakkausar suka a kan yadda Inyamurai suke ta kashe ‘yan Nijar da ke zaune a kasashen Inyamurai, har da fille musu kai.
Suka ce a Nijar ba ka isa ka taba lafiyar wani Inyamuri ba, sai ka shiga uku wajen hukuma. Amma sai ga Inyamuri yana kashe ‘yan Nijar har da fille musu kawuna a Nijeriya, kuma hukumomin Nijar sun yi shiru.
Wani bayani yana cewa gaskiya rashin biyan malaman jami’a albashi har tsawon kusan wata shida, ya jefa su cikin mawuyacin hali tare da iyalansu.
A jihar Barno, ‘yan ISWAP sun kashe wasu mayakan Boko Haram su takwas.
A jihar Bauci, gwamnatin jihar ta rada wa jami’arta ta jihar sunan Sa’adu Zungur wato Sa’adu Zungur Unibersity.
A jihar Katsina, masu fashin jama’a sun yi fashin ango da amaryarsa, sannan suka kashe mutum guda.
TALATA
A karshe dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saki Dariye da Nyame daga gidan yari na Kuje da ke Abuja. Sakamakon karin kudin haraji da Gwamnatin Tarayya ta yi wa kamfanonin sadarwa, kudin kira da na data za su karu da kashi 100.
Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka WAEC, ta fitar da sakamakon jarabawarta ta bana/2022, inda kashi 76 cikin kashi 100 da suka rubuta jarabawar suka ci.
Gwamna Ortom na jihar Binuwai, ya rubuta wa shugaban kasa Buhari neman izinin bai wa ‘yan bijilante na jiharsa bindiga don taimaka wa tsaro a jihar.
Ma’aikatan kamfanin raba wutar lantarki wato DISCOs na Kano, sun ba kamfanin wa’adin mako biyu, ko ya saki kudaden da ake cire musu na fansho ga hukumomin fansho, ko su yi yaji.
Kungiyar Malaman jami’a ASUU shiyyar Kano wacce ta kunshi dukkan jami’o’in da ke jihar Kaduna, da Kano, da Jigawa da sauransu, ta kalubalanci gwamnan jihar Kaduna El-Rufai da ke barazanar korar malaman jami’ar jihar Kaduna, ya nuna wani gini guda daya tal, da ya san shi ya gina shi a jami’ar, a shekara kusan takwas da ya yi yana gwamnan jihar Kaduna.
Ta ce Tetfund/asusun tallafa wa ilimi a manyan makarantu wanda ASUU ce ta yi sanadiyyar kafa shi, shi yake ta gine-gine a jami’ar ba El-Rufai ba.
Jiya Litinin, sabon kwanmandan rundunar soja ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya karbi raganar mulki daga wanda ya gada Manjo Janar Kabir Mukhtar.
Kotu ta sa bakwai ga watan gobe, ta zama ranar sauraron wata kara da aka kai Tinubu, da wanda ya kai karar yake zargin Tinubu ya mika takardun bogi don tsayawa takarar neman shugabancin kasar nan.
Melle Kyari shugaban kamfanin mai na NNPC, ya ce a duk wata, ana sace wa Nijeriya danyen mai na Dala Biliyan Biyu.
A jihar Taraba, masu fashin jama’a sun kashe mutum uku, suka jidi wasu. A jihar Neja, masu fashin jama’a, sun yi fashin mutum uku, suka kashe mutum guda.