Rundunar ‘yansandan Jihar Imo ta cafke wasu mutum uku a yankin Ogii da ke Karamar Hukumar Okigwe bisa zargin mallakar kokon kan mutum.
Wadanda ake zargin sun hada da Patrick Okoere mai shekara 29, da Ifeanyichukwu Anyaemeka mai shekara 28, da Chukwuemeka Onyekachi mai shekara 20, an kama su ne biyo bayan bayanan da mazauna yankin suka bayar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
- Rikicin Uba Sani Da El-Rufa’i Ya Dauki Sabon Salo
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Imo, Henry Okoye ne ya bayyana haka, inda ya ce an kama mutanen uku ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a kan babbar hanyar Okigwe zuwa Umuahia dauke da kokon kan mutum, da kaza, da kuma fararen kaya.
A cewar Okoye, daya daga cikin wadanda ake zargin, Okoere, ya yi ikirarin cewa kawunsa Osunta Oko, shi ne ya bukaci ya sayo kokon kan mutum don amfani da shi akan wani rikicin fili.
Ana zargin ya same shi ne a bakin kogi a wani yanki da ya shahara wajen yin garkuwa da mutane.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ci gaba da kokarin da rundunar ‘yansandan Jihar Imo ke yi na dakile ayyukan ta’addanci a jihar, jami’an shalkwatar sashen Okigwe tare da hadin gwiwar mazauna unguwar Ogii a ranar 3/02/2025, sun kama wasu mutum uku da aka samu da kokon mutum, kaza da fararen kaya a kan titin Okigwe-Umuahia Edpressigwe.
“Mutum ukun da aka kama—Patrick Okoere, Ifeanyichukwu Anyaemeka, da Chukwuemeka Onyekachi 20—ana kan bincike a halin yanzu. Yayin da ake yi masa tambayoyi, Patrick ya bayyana cewa kawun nasa, Osunta Oko, ya nemi ya sayo kokon kan mutum. Ya yi ikirarin cewa ya same shi ne a bakin kogi a kan babbar hanyar Okigwe-Umuahia, yankin da rundunar ke samun labarin sace-sacen mutane.
“Rundunar ‘yansandan Jihar Imo na ci gaba da bin Osunta Oko da sauran masu hannu a cikin wannan lamari mai tayar da hankali. Bugu da kari, ana gudanar da bincike na DNA don sanin ainihin mai kokon.
“Kwamishanan ‘yansandan jihar, CP Aboki Danjuma, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ‘yansandan ta jajirce wajen ganin ta kare lafiya da tsaron daukacin mazauna yankin. Ya kuma jaddada cewa za a yi adalci kuma wadanda ake zargin za su fuskanci hukunci bayan kammala bincike.”