Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad elRufa’i ya bayyana cewa ko gawarsa ba za ta taba kusantar jami’iyyar PDP ba ballanta ya koma cikin jami’iyyar.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a wani martani da yayi wa kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Daniel Bawala ya yi a shafinsa na Tuwita.
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu
A baya, Bwala ya yi hasashen cewa Nasiru el-Rufa’i wanda tsohon minista ne na Babban Birnin Tarayya (Abuja) a karkashin jam’iyyar PDP, zai fice daga jam’iyyar APC mai mulki nan ba da jimawa ba zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Bwala wanda har a kwanan baya dan jam’iyyar APC ne ya ce yana da kwarin gwiwar cewa el-Rufai zai shigo PDP kafin zaben 2023.
Sai dai a martanin da ya bayar a shafinsa, Malam Nasiru el-Rufa’i ya tabbatar wa duniya cewa yana nan daram a jam’iyyar APC ko gawarsa ba za ta kusanci PDP ba.