Tun bayan da hukumar zabe ta Jihar Neja (NSIEC) ta fitar da jadawalin zabukan kananan hukumomin Neja aka fara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin gamayyar jam’iyyun siyasa da majalisar dokokin jihar.
Kamar yadda hukumar zaben NSIEC ta fitar jadawalin zaben zai kasance ne farkon watan Nuwanba, wata uku kafin babban zaben 2023.
- Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
Wanda jadawalin zaben bai yi wa wasu ‘yan siyasa dadi ba, inda aka rika shirya taruka kan kiran gwamnatin jiha ta janye kudurinta na zaben a daidai wannan lokacin.
Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Bosso, Hon. Malik Madawaki Bosso ya gabatar da kuduri ga majalisar, inda ya nemi majalisar da dakatar da hukumar zaben ta jiha kan zaben bisa wasu dalilan doka.
Da yake bayyana matsayar majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Abdullahi Bawa Wuse, ya nemi gwamnatin jiha da ta dakatar da hukumar zaben na kudurin gudanar da zaben wanda ya zo daidai da sashe na ashirin (20) na dokar zaben kananan hukumomi na shekarar 2002 da sashe na ashirin da tara (29) (1) na dokar zabe na 2022.
Kudurin da dan majalisar Madawaki ya gabatar ya ce wa’adin shugabannin kananan hukumomi zai kare ne ranar 12 ga watan Disambar wannan shekarar.
Dan majalisar ya ce jadawalin zaben da hukumar zaben ta jiha ta fitar domin fara shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a jihar, wanda ta tsara zaben fitar da gwani zai kasance tsakanin ranar 20 zuwa 27 ga watan Agusta, inda kuma ta ce za a gudanar da zaben ranar 5 ga watan Nuwamba ya saba wa dokar zaben jiha.
Ya kara da cewar tsakanin ranar 27 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Nuwamba kwana 35 ne, ya ce dokar ta tanadi cewa tsakanin zaben fid da gwani da babban zabe kwanaki dari da tamanin (180) ne.
Dan majalisar ya ce dokar da ta samar da matsayin kananan hukumomi na 2002, ita ce ta haifar da dokokin zaben 2022 da majalisar dokokin jiha ta gabatar kuma ya zama dokar zabe kananan hukumomi a Jihar Neja da wadda aka gabatar a shekarar 2002 da ta 2001.
Madaki ya ce sashi na ashirin (20) na dokokin zaben kananan hukumomi na 2002, ya bayyana za a samar da shugabannin kananan hukumomi ne bisa tsarin zabe da kuma tabbatar da cewar an bi tsarin doka kamar yadda sashi na sha tara (19) ya tanada.
Ya kara da cewar sashi na 29 sakin layi na daya na dokar zabe 2002, ya ce ba wata jam’iyyar siyasa za ta shiga zabe kasa da kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani da babban zabe, sai sun mayar wa hukumar zabe sunayen wadanda suka samu nasarar zaben fid da gwani.
Ya ce a bayyana take cewar NSIEC za ta gudanar da zaben ba bisa doka ba idan ta ci gaba da shirya yunkurin gudanar da zaben a wannan lokacin kamar yadda ta fitar da jadawalin zaben.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban gamayyar jam’iyyun siyasa sha takwas “IPAC” da ke yunkurin shiga zaben, Malam Muhammad Bello Maikujeri, ya ce ‘muna nan kan matsayanmu na shiga zaben kamar yadda NSIEC ta fitar jadawalin zaben.’
Ya ci gaba da cewa majalisar ce ta yi sabon kudurin da ya bai wa shugabannin kananan hukumomi wa’adin shekaru uku kan karagar mulki, sanin kowa ne shugabannin kananan hukumomi na yin wa’adin shekaru biyu ne, amma bayan wannan dokar kotu ta tabbatar wa shugabannin kananan hukumomi wa’adin shekaru ukun, kuma wa’adin mulkinsu zai kare ne a ranar 12 ga watan Disamba.
Ya ce, “Saboda haka daga ranar 12 ga watan Disamba dole ne su sauka, amma ita majalisar dokokin jiha da ke tayar da jijiyoyin wuya ta manta cewa ita ce ta yi dokar, kuma a sabon dokar da muke amfani da shi da ya bai wa shugabannin kananan hukumomi wa’adin shekaru uku, ba ta bayyana gwamnatin rikon kwarya ba. “Idan ta natsu da kyau, hukumar zabe ta NSIEC ta yi abin da ya dace, domin ba zababbiyar gwamnatin karamar hukuma da za ta mika mulki hannun wani kantoma ko rikon kwarya bisa yadda suka tsara dokar.
“Saboda haka, wannan ba hurumin majalisar dokokin jiha ba ne, kotu ce kawai za ta iya warware abin da sabon dokar ya kunsa.
Mu IPAC, mun gamsu kuma mun amince jam’iyyu su ci gaba da shirye-shiryen zaben kananan hukumomi, domin muna magana ne a kan doka ba ra’ayin wani ba.
“Dokar zaben Jihar Neja ba ta samar da wani sashen rikon kwarya ko mika mulki ga wani a karamar hukuma ba, sai dai zababben shugaba. A yau mun ziyarci shugaban hukumar zabe ta Jiha Neja (NSIEC), Alhaji Aminu Baba domin bayyana masa matsayin IPAC a kan wannan takaddamar, mun tsaya ne a kan shiga zabe, kuma mun umurci sauran jam’iyyu su ci gaba da shirye-shiryen fuskar zaben kananan hukumomi na ranar 5 ga watan Nuwamba kamar yadda jadawalin NSIEC ta tsara.