Jarumar masana’antar fina-finai ta Kannywood, Maryam Muhammad, wadda aka fi sani da Maryam Malika, ta roƙi wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna da ta tabbatar da sakin auren da tsohon mijinta, Umar ya yi mata.
Jarumar, wadda lauyanta A.S Ibrahim ya wakilta ta shaida wa kotun, jiya Laraba cewa wanda ake ƙara ya furta saki na uku tun shekaru biyar da su ka gabata bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i (mace ta nemi saki a Musulunci).
- Maryam CTV Ta Nemi A Dinga Nuna Al’adun Bahaushe Maimakon Na Wasu Kasashen Waje A Fina-finan Kannywood
- Ci Gaban Masana’antar Kannywood: Ganin Kitse Ake Wa Rogo – Mai Sana’a
Wadda ni ke karewa ta cigaba da al’amuranta na yau da kullum ba tare da zuwa kotu ba, bayan da tsohon mijin nata ya rubuta saki na uku akan takardar da kotu ta aike masa
kamar yadda Lauya AS Ibrahim ya faɗawa Alkali.
Wanda ake tuhuma ba ya cikin kotu kuma bai aika da wani wakili ba a lokacin da alƙalin kotun, Kabir Muhammad, yake gudanar da zaman shari’ar.
Haka zalika wanda ake ƙara ba ya gida a lokacin da aka je kai masa takardun umarni daga kotun kamar yadda Masinjan kotun ya tabbatarwa alƙali.
Alƙalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aikewa wanda ake ƙara takardar umarni ta wasu hanyoyin sannan ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.