Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada aniyar kasar Sin, ta ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje.
Wang Wenbin, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, yana mai cewa, duk irin sauyin yanayi da za a samu, Sin ba za ta sauya aniyar ta a wannan fage ba.
A kwanan nan ne cibiyar bunkasa cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin ko CCPIT a takaice, ta fitar da sabon rahoto game da yanayin kasuwanci na kasar Sin ta bangaren jarin waje, wanda ya nuna irin yadda kamfanoni da yawa masu jarin waje, ke da kyakkyawan fata game da makomar bunkasar kasar Sin cikin dogon lokaci.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa mai nasaba da wannan batu, Wang Wenbin ya ce Sin na da imanin cewa, a yayin da ake zurfafa aiwatar da matakai na kandagarkin annoba, tare da gudanar da ayyuka na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, tattalin arzikin kasar zai kara nuna yanayinta na jure kalubale.
Ya ce Sin za ta ci gaba da bude kofofin ta ga sassan duniya, za ta kyautata muhallin kasuwanci ga kasashen waje, ta yadda za su kara zuba jari, tare da bude kasuwanci a kasar Sin, su kuma yi aiki tare domin kara dunkulewa, da cimma karin nasarori a nan gaba. (Saminu Alhasan)