Yar uwa ki jika abu kaza da kaza ki sha domin ki fitar da zakin dake mararki kafin nakudar haihuwa, ko kuwa wane karbi wannan maganin ka kai wa iyalinka ka ce ta jika ta rika sha maganin zaki ne.
Wadannan su ne irin maganganun da za ka ji suna zagawa musamman tsakanin Mata in sun hadu da mai juna biyu. To amma fa mu a likitance ba mu san wani abu wai shi zaki a marar mace ba ballantana fitarsa a jikin mace mai gabatowar haihuwa.
Duk da irin wannan al’ada ta jima amma duk da haka mun shigo wani zamani yanzu da gurbatattun labarai da bayanai marasa sahihanci na ilimi suka yawaita kuma ke kai komo tsakanin al’umma cikin kafafen sadarwa iri-iri.
Komai mutane suka ji ba duk ke tsayawa su yi nazari da binkice ba akan;
Shin kaza din nan da aka ce ya ma dace da ni kuwa?
Sannan dadin abin aka fada amma mene ne illar da ka iya biyo bayansa? Shin hakan ma batun yake a ilmance ko kuwa?
Wannan ta sa da zarar haihuwa ta gabatowa mace kowa sai ka ga shawara yake ba ta akan komai ma, musamman ma atsakaninsu mata, Eh munsan kuna yi ne bisa kyakkyawar manufa da son ku ga ta haihu lafiya, amma fa ba duk ‘yan’adam bane zubin halittarsu tare da komai yai daidai da na juna ba.
Ba mamaki wata kuka ji ta yi irin haka ta wanye lafiya, amma mu tuna fa idan wani ya yi abu ya kwana lafiya to fa wani in ya yi wahala zai sha.
Babu wani abu da sunan zaki jikin mai juna biyu, in aka ce zaki a jika to fa mu ko yaushe a likitance abin da muka sani; ana batu ne na ciwon suga ajikin mutum, wato yawaitar sinadarin Bulkodi a cikin jini.
Shi ko ciwon suga yayin goyon ciki, kuma muddin aka gano shi ba’a wata-wata ake dora mace kan shawarwarin abinci ko magunguna wasu lokutan allura domin ba ta kariya daga hatsarin suga da ka iya tasowa, wanda cikin irin wannan hatsarin akwai mutuwar jariri a ciki, mutuwar macen wajen haihuwa, zubewar ciki, ko sanya jariri ya yi girma fiye da kima a ciki ta yadda ba zai iya fitowa ba sai dai ai aiki a ciro shi, ko kuwa sai an kara fadin wajen kafin kan jariri ya iya wucewa.
Wasu kan dauki kowanne katoton jariri lafiya ce tasa, amma ina wani girman ba na ka’ida bane larura ce, galibi alama ce ta larurar suga yayin goyon ciki a uwar musamman a macen da ba ta rika zuwa awo ba, ko kuwa ba ta samu duk gwaje-gwajen da suka dace ba, kurum an auna arziki ne. Duk jaririn da nauyinsa ya wuce kilogiram 3.5 lafiyar mahaifiyarsa abin tuntuba ce a yayin goyon cikinsa.
Shi kuwa wannan sugan ajini yake ba zai taba fita ta ta gaban mace ba ko ta hanyar fitar da wani ruwa ba.
Za Mu Ci Gaba A Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu