Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama wani da ake zargi da satar waya, ana zargin ɗan kungiyar ‘Shila’ ne, bisa laifin fashi da makami a ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa. Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, CP Danwambo Morris, ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne bayan wani ƙorafi da Hadiza Atiku daga Wuro harɗe ta shigar.
Bisa ga bayanan Ƴansanda, wanda ake zargin mai suna Usman Abubakar, ya kai wa Hadiza hari, inda ya soke ta a fuska da almakashi sannan ya kwace mata wayarta ƙirar Infinix WOD 9. Wannan hari ya janyo wa matar munanan raunuka, wanda hakan ya sa ta garzaya wajen jami’an tsaro don neman agaji.
- Shahararren Malamin Addinin Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
- Ƴan Bindiga Sun Sace Fastoci 2 A Adamawa
Bayan samun rahoto, jami’an Ƴansanda daga ofishin Mubi ta Arewa sun gaggauta ɗaukar mataki, inda suka bi sawun wanda ake zargi kuma suka samu nasarar cafke shi.
Bincike ya nuna cewa yana da hannu a wasu ayyukan fashi da makami, kuma an kwato kayayyakin da aka sace daga hannunsa, ciki har da keke Napep, da wayar salula, da kuma Almakashi da ya yi amfani da shi.
Kwamishinan Ƴansandan ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannun hukuma yana kuma taimakawa a bincike. Ya ce za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike, tare da jaddada ƙudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Adamawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp