Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata ta zargin da ke cewa yana shirin yin takarar shugaban ƙasa a 2031, yana mai cewa hankalinsa yana kan harkokin tsaro da nasarar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, yana mayar da martani ga kalaman da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi a wata hira da aka yi da shi a daren Litinin.
- Za Mu Tabbatar Da Tsaro Tare Da Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya – Nuhu Ribadu
- Gwamna Uba Sani Da NSA Ribadu Ba Abokaina Ba Ne — El-Rufai
Ya ce ba zai shiga rikici da El-Rufai ko kowa ba, tare da jaddada cewa duk da munanan kalaman da aka yi a kansa a baya, bai taɓa sukar tsohon gwamnan ba.
“Don kauce wa ruɗani, ina so in fayyace cewa ban taba tattauna batun yin takarar shugaban ƙasa a 2031 da kowa ba. Hankalina gaba ɗaya yana kan ci gaban Nijeriya da kuma nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu,”
in ji Ribadu.
Ya buƙaci jama’a su yi watsi da kalaman El-Rufai, tare da kira ga tsohon gwamnan da ya kyale shi ya mayar da hankali kan aikinsa na ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp