Mutane sama da dubu 500,000 ne za su amfana da tallafin abinci na Ramadan a faɗin Jihar Zamfara, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙauran Namoda da Birnin Magaji, Hon. Sani Jaji, ya ƙaddamar.
Ko’odinatan jihar na shirin Jajiya Amana, Hon. Aliyu MC, ne ya bayyana hakan yayin taron ƙaddamar da shirin a Gusau, babban birnin jihar.
- Fitaccen Fim Din Na Kasar Sin Mai Suna “Ne Zha 2” Ya Zama Na 7 A Jerin Fina-finai Mafi Samun Kudi A Duniya
- Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
Hon. Aliyu MC ya ce waɗanda za su ci gajiyar shirin sun haɗa da marayu, da zawarawa, da masu buƙatu na musamman, da matasa, da mambobin jam’iyyar APC a faɗin jihar. Haka nan, an kafa cibiyoyi 41 domin dafa abinci da raba shi ga al’umma har zuwa ƙarshen watan Ramadan.
A nasa jawabin, Hon. Sani Jaji ya ce tallafin na daga cikin ƙoƙarinsa na rage wa al’umma raɗaɗin halin da ake ciki da kuma neman lada a wannan wata mai alfarma. Ya ƙara da cewa rashin bin dokokin shari’ar Musulunci ne ya jefa ƙasar cikin halin matsin rayuwa, don haka sai an koma ga Allah sannan za a samu mafita.
Shugaban jam’iyyar APC na ɓangaren Jajiya Amana, Hon. Ishaka Ajiya, ya gargaɗi waɗanda aka ba alhakin raba abincin da su ji tsoron Allah, inda ya yi alƙawarin ɗaukar mataki kan duk wanda aka kama da almundahana a shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp