Hukumar Zaɓen Jihar Ribas (RSIEC), ta sanar da cewa za ta gudanar da sabon zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 9 ga watan Agusta.
Shugaban hukumar, Adolphus Enebeli ne, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Fatakwal a ranar Laraba.
- Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
- Afirka Na Da Wata Abokiya Da Za Ta Iya Dogaro Da Ita
A ranar Larabar da ta gabata ne, Kotun Ƙoli ta ta soke zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar bisa hujjar cewa an samu kura-kurai a tsarin zaɓen.
Wannan hukunci ya haifar da buƙatar gudanar da sabon zaɓe domin cike gurbin shugabancin ƙananan hukumomin jihar.
Bugu da ƙari, majalisar dokokin jihar ta gayyaci shugaban hukumar zaɓen, Adolphus Enebeli, don ya bayyana a gabanta domin yin bayani kan shirin sake zaɓen da kuma matakan da aka ɗauka don tabbatar da ingantaccen zaɓe mai zuwa.
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe.
Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp