Hukumar EFCC a Kano ta samu nasarar gurfanar da wata mata, Hauwa Abdullahi Ibrahim, kan laifin shigo da dala $1,154,900 da Riyal 135,900 daga Saudiyya ba tare da sanar da hukumomin Nijeriya ba.
Kotun ƙarƙashin mai shari’a S. M. Shuaibu, ta yanke mata hukunci bayan ta amsa laifin safarar kuɗin ba bisa ƙa’ida ba.
- Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Tiktok 2 Kan Yaɗa Kalaman Batsa A Kano
- Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su
An kama Hauwa ne a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) ta hannun jami’an Kwastam, inda suka miƙa ta ga EFCC domin ci gaba da bincike da shari’a.
A cikin kotu, Lauyan EFCC, Musa Isah, ya gabatar da shaidun kuɗin da aka kama, yana mai buƙatar kotu ta yanke mata hukunci bisa amsa laifinta.

Alkalin kotun ya umarci a kwace kuɗin tare da mika su ga gwamnatin tarayya, bisa tanadin dokar hana safarar kuɗaɗe ta shekarar 2022.














