“A matsayinsu na manyan kasashe, Sin a bangaren masu tasowa da Amurka a bangaren masu ci gaba a duniya a yau, dukkan kasashen biyu za su dade a wannan duniyar, don haka dole ne su zauna tare cikin lumana.” Irin haka ne mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana ma’anar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, yayin wani taron manema labarai a game da taken diflomasiyya na manyan tarukan kasar Sin guda biyu.
To, shin yaya dangantakar Sin da Amurka? Batun mutunta juna da cin gajiyar juna dai su ne galibi ra’ayoyin masu ba da amsa suka zo daya a kai, kamar yadda wani bincike da kafar yada labarai ta CGTN mallakin hukumar rukunin gidajen rediyo da talabijin ta kasar Sin ta gudanar a tsakanin matasa 4,003 masu shekaru 18 zuwa 45 a kasashen Sin da Amurka.
- Kotu A Kano Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Kan Safarar Maƙudan Kuɗaɗe
- Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya
A wurin taron manema labarun, yayin da ake kimanta takaddamar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, Wang Yi ya tambayi Amurka cewa, “Mece ce ribar da za ta samu daga yakin haraji da kuma yakin cinikayya? Shin gibin ciniki yana karuwa ne ko raguwa? Shin masana’antu sun matsa kaimin yin gasa ko kuma gwiwarsu ta yi sanyi? A cikin binciken ra’ayoyin, matasan da suka amsa tambayoyi daga kasashen biyu sun yi imanin cewa, cin gajiyar juna, shi ne tushen warware batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, kuma kashi 87.3 cikin dari na Sinawa da kashi 78.5 na matasan Amurkawa sun amince da wannan ra’ayi.
A yayin da ake kimanta dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, kashi 66.4 cikin dari na matasan kasar Sin da suka bayyana ra’ayoyi sun zabi “hadin kai da gasa”, kuma kashi 17.7 cikin dari daga cikinsu suna tunanin “gasa ce” ta fi. Sai kuma kashi 43.1 cikin dari na matasan Amurka da suka amsa cewa sun zabi “dorewar hadin gwiwa da gasa”, kuma kashi 22.7 daga cikinsu suka zabi “alaka ta yin gasa.” Masu bayyana ra’ayoyin sun yi kira ga kasashen biyu da su natsu su kalli tsarin matsalolin da ake fuskanta a dangantakar tattalin arziki da cinikayya, kana su tsayu a kan tattaunawa tare da warware su yadda ya kamata.
CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da wannan bincike na ra’ayoyi ta hannun Cibiyar Nazarin Sadarwa ta Duniya A Sabon Zamani, da niyyar gudanar da binciken a tsakanin matasa masu shekaru 18 zuwa 45 daga Sin da Amurka. Samfurin tambayoyi da aka yi ya dace da shekaru da jinsi na yawan matasan da aka tambaya masu shekaru 18 zuwa 45 a kasashen biyu. Binciken ya karade dukkan jihohi 50 na Amurka da birnin Washington D.C., kuma a kasar Sin, ya karade manyan birane 16 na yankuna bakwai, da suka hada da Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Chengdu, da Xi’an. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp