A dai dai lokacin da gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar samar da wani sabon tsari na makamashi, wanda motoci za su dinga amfani da injin gas na CLG da LNG wanda bashi da illa wajen gurbata muhalli.
Samar da motocin sufuri na Bus da kungiyar masu motocin sufuri da daukar ma’aikatan na kasa wato RTEAN wanda ta yi masu anfani da iskar gas na CLG da LNG, na daga cikin muradun gwamnatin tarayya na bunkasa sufuri a kasar nan.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Nasarori Da Matsalolin Da NAHCON Ke Samu Wajen Gudanar Da Aikin Hajji
A kan haka aka gudanar da gagarumin taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin sufuri. Wannan kuma yana zuwa ne dai dai lokacin da gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar cire tallafin man fetur.
Tuni dai kungiyar RTEAN karkashin jagorancin Dakta Musa Muhammad Maitakobi ta kuduri aniyar zama sahun gaba wajen canza fasahar motocin ta domin anfani da iskar gas ta CLN da LNG.
A tattaunawarsa da wakilimu, Alhaji Musa Maitakobi ya ce, “Yana da muhimmancin gaske anfani da iskar gas na CNG LNG a motocinmu, kungiyarmu a matsayin ta na babban mai ruwa da tsaki kan harkokin sufuri a Nijeriya ta zama sahun gaba wajen soma amfani da fasahar wajen juya motocinta masu anfani da fetur da diesel zuwa fasahar gas ta CNG da LNG”.
“Abin da za a maida hankali akai shi ne amfani da iskar gas mai dauke da sinadarin mythane, kamar albarkatun iskar gas da na LPG musamman ganin Allah ya huwace wa Nijeriya wannan albarkatun na iskar gas mai yawan gaske.
” Ya kuma kara da cewa, “A shirye muke mu samar da mafita ga matsalar makamashi wanda in aka aiwatar dashi za a samu natija kwarai da gaske kuma zamu yi aiki kafada kafada da ma’aikatar mai fetur ta kasa.
” Ya kuma ce, “Bisa ga hasashen mu muna da masaniyar cewa mutane da daman gaske ne za su iya yin canjin fasaha daga anfani da man fetur da diezel zuwa amfani da iskar gas na CNG da LNG, Kuma gwamnatin tarayya ta shirya tsaf a don ganin wannan Shirin ya yi nasara ina baku tabbacin cewa ba za a fuskanci karanci, ko tashin farashin iskar ga din ba.”
Alhaji Musa Maitakobi ya kuma karkare da cewa, “Kamar yadda aka yi yarjejeniya birnin Faris na tsaftace muhalli daga gurbacewa. Lallai akwai bukatar yin anfani da makamashi mai tsafta wanda ba zai gurbata muhalli ba.”
Gwamnatin tarayya dai ta kuduri aniyar juya motocin sufuri akalla Miliyan biyar daga amfani da fasahar man fetur da diezel zuwa amfani da iskar gas na CNG da LNG a karkashin wannan sabon shirin, kuma za a samar da tashoshin makamashin iskar gas a sassa daban daban na fadin kasar nan.