Wani yaro ɗan shekara 14 ya rasa ransa, yayin da mutum 21 suka jikkata sakamakon fashewar gas a unguwar Goron Dutse da ke Kano.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:30 na rana a gidan Malam Isiyaka Rabiu, lokacin da wata tukunyar gas ta fashe a cikin ɗakin girki.
- Zelensky Ya Ziyarci Saudiyya Don Kawo Ƙarshen Rikicin Ukraine Da Rasha
- Tambuwal Ya Tallafawa Magidanta Dubu 30 Da Kayan Abinci
Fashewar ta haddasa gobara wacce ta kama wasu sassa na gidan kafin jami’an agajin gaggawa su shawo kanta.
Jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagorancin ACP Nuhu Mohammed Digi na yankin Dala, sun isa wajen tare da jami’an kashe gobara don daƙile lamarin.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin Gamji, Asibitin Ƙashi na Dala, da Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed domin ba su kulawa.
Hukumomi sun tabbatar da cewar lamura dun daidaita a yankin, yayin da ‘yansanda suka miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp