Manyan jami’o’in kasar Sin da dama sun bayyana shirin fadada daukar daliban digiri na farko a shekarar 2025, tare da mai da hankali sosai kan manyan tsare-tsare na kasa da fasahohin zamani.
Jami’o’in Tsinghua da Peking sun ba da sanarwar shirin kara yawan daliban digiri na farko da za su dauka zuwa kusan 150 kowannensu. Jami’ar Tsinghua za ta kafa sabuwar kwalejin ilimi ta gaba daya don mai da hankali kan habaka hazaka a fannonin ilimi daban daban na kirkirarriyar basira (AI). Haka ma sabon shirin shiga jami’ar Peking zai mai da hankali ne kan fannonin bukatu na manyan tsare-tsare na kasa, da muhimman fannoni, da sabbin bangarori masu tasowa.
- Kamfanin Kasar Sin Zai Gudanar Da Aikin Farfado Da Muhallin Halittu Na Kogin Nairobi Na Kasar Kenya
- Barcelona Ta Tsallaka Zuwa Matakin Kwata Fainal A Gasar Zakarun Turai
Kazalika, Jami’ar Renmin za ta kara ba da damammakin shiga jami’ar sama da 100 a fannoni kamar su AI. Haka ma sauran jami’o’i, irin su Jami’ar Shanghai Jiao Tong da Jami’ar Wuhan, za su fadada fannoni a AI, da makamashi da ake sabuntawa, da kuma kwakwalen na’urori na sassan kayayyakin laturoni don biyan bukatun kasa da kasa.
Rahoton aikin gwamnatin Sin na shekarar 2025 ya jaddada mahimmancin ci gaba da habaka shirin “AI Plus”, da nufin hada fasahar dijital tare da karfin masana’antu da na kasuwa. Rahoton ya ba da shawarar yin amfani da fasahar Large Language models da bunkasa hajojin masu alaka fasahar zamani na gaba.
A watan Janairu ne kasar Sin ta fitar da shirinta na farko na kasa don gina “kasa mai karfin ilimi” ya zuwa nan da shekarar 2035, don taimakawa daidaita ci gaban ilminta, da kara ingancin kirkire-kirkire, da gina “kasa mai karfi.” (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp