Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya karɓi ragamar rundunar bayan naɗin da Hukumar ‘Yansanda ta Ƙasa, ta amince da shi.
Ya maye gurbin CP Salman Garba Dogo, wanda aka ɗaga matsayinsa zuwa mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda (AIG).
- Manyan Jami’o’in Kasar Sin Sun Fadada Daukar Dalibai A Fannin AI Da Manya Tsare-tsare
- Matsin Amurka Ya Zama Zaburarwa Ga Kasar Sin Wajen Kara Samun Ci Gaba
Kafin wannan naɗi, CP Bakori ya riƙe muƙamin kwamishinan ‘yansanda mai kula da sashen binciken kisan kai a hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja.
Yanzu, zai jagoranci ƙoƙarin tabbatar da tsaro da rage aikata laifuka a Kano, wacce ke fama da matsalolin daba, fashi da makami, ƙwacen waya, da rikicin masarauta da ya janyo cece-kuce.
Shugaban hukumar ‘yansanda mai ritaya, DIG Hashimu Argungu, ya buƙaci sabon kwamishinan da ya mayar da hankali kan samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Ya kuma yi kira a gare shi da ya fuskanci ƙalubalen tsaro da ke Kano tare da ɗaukar matakan da suka dace don daƙile matsalolin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp