Majalisar Dattawa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Gwer ta Yamma da ke Jihar Binuwai.
Majalisar ta ce yin hakan zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin, musamman saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
- Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
- Barcelona Ta Tsallaka Zuwa Matakin Kwata Fainal A Gasar Zakarun Turai
Sanata Tartenger-Zam daga Binuwai ne ya gabatar da ƙudirin a zaman majalisar na ranar Laraba, inda baki ɗayan ‘yan majalisar suka amince da bu5katar.
Sanatan ya koka kan yadda jami’an tsaro ke yin jinkiri wajen kai ɗauki duk lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari, musamman waɗanda ke iƙirarin makiyaya ne.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi da Litinin da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Gwer, inda suka kashe mutum huɗu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp