A ranar 4 ga watan Fabirairun 2025 ne, Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet), ta kaddamar shirin hasashen yanayi na daminar noman bana (SCP).
Shirin, wanda hukumar ta kaddamar da a Abuja, wanda kundin hukumar da ta kaddamar ya nuna cewa, daukacin sassan kasar nan, za a samu ruwan sama mai yawan gaske, wanda kuma zai iya sauka tun kafin lokacin da ya kamata ya fara sauka.
Wani kwararre a fannin aikin noma, Cif Dennis Denen Gbongbon, ya sanar da cewa; akasarin manoma a yankin Arewa ta tsakiya, sun dogara ne ga saukar ruwan sama, wanda kuma za a iya samun jinkiri wajen saukarsa, inda ya ce, dole ne manoma su rika kula da tsarin sauyin lokaci.
- Tsohon Firaministan Lebanon: Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba
- Sakamakon Neman ’Yancin Taiwan Zai Kai Yankin Ga Halaka
Shi kuwa, wani kwararren a fannin ‘Teryima Iorlamen’, ya yi nuni da cewa, gyaran kasar noma da sauran saukar ruwan sama kafin a yi shuka, na da muhimmancin gaske ga manoma.
Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Delta, Bayelsa, Ribas da Anambra da kuma wasu sassan Jihohin Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Enugu, Imo da kuma Ebonyi, za su fara samun ruwan sama mai yawangaske.
Kazalika, hukumar ta yi hasashjen cewa; za a iya samun jinkirin ruwan sama a jihohi kamar irin su Filato, Kaduna, Neja, Biniwe, Nassarawa, Taraba, Adamawa da kuma Kwara.
Bugu da kari, a wasu sassan jihohi kamar su; Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, hukumar ta ce; ana sa ran samun saukar ruwan sama a farkon damina.
Sai dai, hasashen hukumar ya bayyana cewa; a wasu sassan Jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi, Anambra da kuma Enugu, za a iya samun jinkirin saukar ruwan saman a kakar noman ta bana.
Saboda haka ne, hukumar ta shawarci manoman da ke da ra’ayin noma a kakar noman ta bana da su tabbatar sun tuntube ta, ko kuma tuntubar sauran hukumomin da ke hasashen yanayi, domin sanin lokacin da ya ya fi dacewa su yi shuka.
Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, za su fuskanci daukewar ruwan sama da wuri, inda aka kwatanta da na dogon zango da aka samu a daminar bara.
Haka zalika, hukumar ta yi hasashen cewa; za a samu jinkirin ruwan sama a wasu sasssan jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi, Anambra da kuma Enugu.
A cewar Hukumar, mai yiwuwa kakar daminar ta bana ta kasance gajera a wasu sassan Jihohin Borno da Yobe, sabanin yadda aka saba gani.
Hukumar ta yi hasashen cewa, mai yiwuwa kakar daminar ta bana, ta yi tsawo a Jihohin Legas da Nasarawa, sabanin yadda aka saba samu.
Hukumar ta yi hasashen cewa, daga watan Mayu zuwa na Yuni, za a samu ruwan sama kamar da baakin kwarya, wanda kuma mai yiwuwa, a samu afkuwar ambaliyar ruwa a wasu biranen da ke kusa da rafuka a kasar.
Kazalika, daga watan Afirilu zuwa na Mayu, yankunan Saki, Iseyin, Ogbomoso, Atisbo, Orelope, Itesiwaju, Olorunsgo, Kajola, Iwajowa da kuma Oro Ire da ke cikin Jihar Oyo, an yi hasashen samun karancin ruwan sama, wanda zai iya kai wa har tsawon kwana 15, bayan saukar ruwan saman.
Bugu da kari, Hukumar ta yi hasashen cewa; a wasu jihohin da ke Arewacin kasar nan, daga watan Yuni zuwa Yuli har zuwa watan Agustan 2025, za a samu karancin ruwan sama, wanda zai kai har tsawon kwana 21, inda kuma a Jihohin Ekiti, Osun, Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Anambra, Imo, Abia, Kuros Riba, Delta, Bayelsa da kuma Akwa Ibom, za a samu ruwan sama na tsaka-tsaki da zai kai kwana 15.
Daga tsakanin kwana 27 zuwa 40, za su shige ba tare da wani batun hasashe samun sauyin yanayi ba, haka za a fuskanci rani kadan a yankin Kudu Maso Gabas daga ranar 22 na 2025.
Saboda haka ne, kwararru a fannin aikin noma suka shawarci manoman kasar nan, musamman wadanda ke jihohin da ke tsakiyar kasar, da su tabbar da sun yi shuka da Irin da ke jurewa kowanne irin yanayi, musamman domin kauce wa fuskantar matsalar rashin samun saukar ruwan sama a kan lokaci a kakar noman ta 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp