• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI

by Abubakar Abba and Sulaiman
8 months ago
Nama

An rattaba hannun yarjejeniya tsakanin Mayankar dabbobi ta Jurassic da kuma Shirin Bunkasa Kaya (CDI), domin a rika fitar da nama zuwa kasuwar Saudiyya.

Wannan yarjejeniya mai matukar muhimmanci, ta saita Nijeriya wajen kokarin kara samar da wadatacce kuma ingantaccen nama da za a rika fitar da shi zuwa Kasar Saudiyya.

  • Na Cire Tallafin Mai Ne Domin Kare Makomar Matasan Nijeriya —Tinubu
  • Kudirin Hana INEC Yin Rajista Da Daidaita Lamuran Jam’iyyu Ya Tsallake Karatu Na Biyu

A karkashin wannan yarjejeniya, mayankar Jurassic, za ta samar da nama, inda kuma shirin CDI, zai tabbatar da samar da kasuwa, ta hanyar yin hadaka da kamfanin noma da zuba hannun jari kan dabbobi (SALIC), tare da masu fitar da naman masu zaman kansu da ke Saudiyya.

Manajan Darakta na Kamfanin ‘P and I’, wanda shi ne ke jagorantar mayankar Jurassic, Dakta Anyebe Idoga ya sanar da cewa, wannan yarjejeniyar na da matukar muhimmanci.

“Wannan shiri, ya zo kan gaba tare da yi wa ‘yan Nijeriya amfani, duba da cewa; za mu yi aiki kafada da kafada da gwamnatin taraya da na jihohi, musamman don kara bunkasa zuba hannun jari, inda hakan zai bayar da damar samar da wadataccen nama a kasuwar duniya, duba da cewa; za a fara gudanar da shirin ne a kasar Saudiyya”, a cewar Anyebe.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare.

“Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh.

Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya.

A yanzu haka, CDI na ci gaba da tattaunawa da SALIC, musamman domin cimma bukatar samar da naman, wanda hakan zai kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.

Wannan hadaka a tsakanin sauran sassan gwamnati daban-daban da CDI ke jagoranta, manufar ita ce; domin fitar da nama ketare kimanin tan 35,200 zuwa karshen 2025.

Bugu da kari, masu ruwa da tsaki a sassan kula da ayyukan kula da dabbobi da kwararrun likitocin dabbobi, duk an sanya su a cikin wannan aiki.

Aikin mayankar na Jurassic, ya kai na dala miliyan 10; wanda kuma ake gudanar da shi a hekta 50 da ke Nasarawa Egon, cikin Jihar Nasarawa.

Ana sa ran, za a kammala wannan aikin a watan Satumban 2025, inda wajen aikin zai dauki yawan Shanun da za a yanka da suka kimanin 1,000 da kuma Akuyoyin da za a yanka a kullum.

Kazalika, aikin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye, sama da 20,000 da kuma ayyukan yi wadanda ba na kai tsaye ba, kimanin 100,000 tare da kara bunka tattalin arzikin Nijeriya da kuma daga darajar Naira.
A shirin fitar da Naman, an kiyasta samar da kudin shiga da ya kai kimanin dala miliyan 273, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 451 kafin zuwa 2025.

Wannan hadakar ta nuna irin kokarin da Nijeriya ke yi, duba da cewa; hakan zai kara wajen ganin ana amfana da fannin na aikin noman, tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Next Post
Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka  – SSANU

Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka – SSANU

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.