Wasu daga cikin tubabbun ‘yan kungiyar ta’adda ta Boko Haram sun roki mazauna jihar Borno da su yafe musu kan ta’addancin da suka aikata musu.
Tubabban sun gabatar da wannan rokon ne a ranar Asabar a garin Maiduguri yayin da suka gudanar da tsaftace wasu tituna a garin Maiguduri.
Cibiyar dabbaka Mulkin Dimokuradiyya da samar da ci gaba dake Nijeriya (CDD) tare da hadakar gwamnatin jihar Borno suka dauki nauyin gudanar da tsaftace titunan.
Tubabban sun gudanar da tsaftace titunan sanye ta Rigunan T-shirts mai dauke da bayanai kamar haka: ‘Mun tuba ku yafe mana, ‘Ya kamata mu sake gina jihar Borno’.
Daya daga cikin jami’an Cibiyar ta CDD, Mala Mustafa wanda ya halarci inda tubabbun ke gudanar da aikin na tsaftace titunan ya ce, wannan na daya daga cikin hanyoyin da zai bai wa tubabbun damar shiga cikin jama’a.
Mala ya ce, daga cikin tubabbun su 400, mutum 50 daga cikin su ne Cibiyar ta dauko don gudanar da aikin na tsaftace titunan.