Hukumar tsaro ta farin kaya ta (NSCDC) a jihar Sokoto, a karshen mako ta baje kolin wasu gaggan masu garkuwa da mutane biyu da suka addabi yankunan Silame, Binji, Gudu, Tureta da karamar hukumar Dange/Shuni a jihar.
Bayan nasarar cafke su, tawagar masu garkuwan sun nemi jami’an tsaron da suke sake ‘yan uwansu, za su ba Jami’an cin hanci na naira miliyan 10.
Da yake magana da ‘yan jarida a Sokoto, Kwamandan hukumar a jihar, Muhammad Dada, ya ce wadanda suka cafke sun hada da Alhaji Koire da Alhaji Buba, sun kasance ‘yan bindiga masu hatsarin gaske da suke da sama da mabiya 300 da suke addabar mutane.
Muhammad ya ce ‘yan ta’addan, “Sun addabi al’ummar Silame, Binji, Gudu, Tureta da karamar hukumar Dange/Shuni da ke jihar.
“Lokacin da na samu labarin inda suke boya a maboyarsu da ke karamar hukumar Silame. Ni da kaina na jagoranci tawagata zuwa can inda muka shafe kwanaki biyu a cikin daji, mun kuma sami nasarar kamo su bisa wannan farmakin da muka kai.
“Bayan da muka kama su ‘yan tawagarsu sun yi kokarin ba mu cin hanci na miliyan 10 domin mu sake wadanda muka kama.”
Daga nan ya sha alwashin cewa za su kara azama da kwazo tare da takwarorinsu na tsaro domin tabbatar da dakile aniyar bata-garin da suka addabi al’umma.
Alhaji Buba, da bakinsa ya ce ya shiga harkar garkuwa da mutanen karamar hukumar Dabegi Dange/ Shuni inda suka amshi kudin fansa na naira miliyan 4 da kuma yin wani garkuwan a Kudula a karamar hukumar Gudu inda suka karbi miliyan 1 na fansa.
Ya ce suna da shugaba a Jamhuriyar Nijar mai suna Danbuzu da yake musu safaran bindiga AK-47 da alburusai.