Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada tsohon hadiminsa a bangaren kafafen sadarwar zamani, Bashir Ahmad, a matsayin sabon babban mai taimaka masa kan fasahar sadarwar zamani.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya tabbatar da nadin a wata wasika da ya aike wa Bashir Ahmad, mai kwanan wata 20 ga watan Yulin 2022.
- Jakadan Morocco: Morocco Tana Martaba “Manufar Sin Daya Tak A Duniya”
- Tubabbun ‘Yan Ta’adda Sun Roki Yafiyar ‘Yan Nijeriya
Mustapha, ya ce nadin zai fara aiki ne nan take tun daga ranar 19 ga watan Yulin 2022.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Bashir Ahmad, dai ya yi murabus daga mukaminsa na hadimin Buhari a fannin kafafen sadarwar zamani domin bin umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa mukarrabansa da suke da sha’awar shiga siyasa da su ajiye mukamansu domin shiga harkokin siyasarsu.
Bashir dai ya sha kaye a zaben fitar da gwani da ya fito neman tikitin tsayawa takarar dan majalisar tarayya mai neman wakiltar mazabar Gaya, Ajingi, Albasu daga Kano a karkashin jam’iyyar APC.
Bayan da aka gudanar da zaben, Bashir ya fito baro-baro ya zargi an masa magudi a zaben tare da kayar da shi da gangan.