Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutum biyu a wani hatsarin mota da ya auku a kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano, kusa da sinimar Eldorado.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safe a ranar 26 ga watan Maris, 2025.
- Wang Yi Ya Gana Da Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasa Na Amurka Mai Lura Da Alakar Sin Da Amurka
- Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya
Ya haɗa da babbar mota ƙirar DAF da kuma babur ƙirar Jincheng, sakamakon tuƙin ganganci.
Daga cikin mutane shida da hatsarin ya rutsa da su, biyu sun mutu yayin da ɗaya ya jikkata sosai.
An kai wanda ya jikkata zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad domin kula da shi, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
FRSC, ta miƙa lamarin ga ‘yansanda don bincike, tare da yin kira ga direbobi su kiyaye dokokin hanya domin guje wa irin wannan hatsari.