A ranar Talatar da ta gabata ne gobara ta kama wani sabon dakin kwanan ɗalibai mata da aka gina a jami’ar jihar Sokoto, lamarin da ya tsorata al’ummar jami’ar.
Gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 3:30 na rana, ta kona ɗaukacin ginin da aka gina kwanan nan domin magance kalubalen ɗakuna da ɗaliban ke fuskanta.
- Wakilin Sin: Dole Ne A Mutunta Hakki Mai Tushe Na Palasdinawa
- Aminu Ado Ya Soke Hawan Sallah Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Kano
Yayin da har yanzu ba a san ainihin musabbabin tashin gobarar ba, ɗalibar da ta yi magana kan lamarin ta ce, “Har yanzun, ba mu san abin da ya tada gobarar ba.”
Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp