Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan Sallah karama Eid-el-Fitr na bana a ranar Lahadi, ‘yan Nijeriya sun gudanar da hidimominsu duk da matsalolin tattalin arziki.
Al’umma na cike da gaisuwar barka da Sallah inda dangi da abokan arziki suke taruwa domin taya juna murna, yayin da aka nuna al’adun gargajiya irin su hawan Sallah a yawancin jihohin Arewa, tare da wuraren shakatawa cike da maziyarta.
- Dantsoho Ya Nemi Masu Zuba Hannun Jari Da Su Ci Gajiyar Tsarin EPT Na NPA
- Ƙarar Kwana: Yadda Hakimin Kaduna, Sarkin Yaƙin Zazzau Ya Faɗi Ya Rasu
Kazalika yawancin iyalai na fama da wahalhalu da suka shafi manufofin tattalin arziki na gwamnati, nagartattun mutane sun kawar da kai ga barin wadannan kalubalen don bikmiin aiwatar da bikin Sallah karama ta bana.
Duk da wadannan kalubalen tattalin arziki da ake fama da su, shugabanni na ci gaba da kira ga al’ummar kasa da su ci gaba da nuna kauna da kyautatawa juna.
A jawabinsa na Sallah, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma tare da jaddada muhimmancin tausayawa da jin kai a wannan lokaci na bukukuwan. Gwamnoni da wasu manyan mutane kuma sun yi wa’azi game da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin ‘yan uwansu.
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan.
A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan, wanda ya hada da koyar da rayuwar soyayya, hadin kai cikin adalci, kula da gajiyayyu da marasa galihu.
Ya jaddada cewa ya zama wajibi a ci gaba da gudanar da rayuwar ibada da tsarki da kuma biyayya ga Allah ko da a bayan Ramadan.
Dakta Salman ya bukaci al’ummar Musulmi da su zauna lafiya, da lumana, da kaunar kasa, ba tare da nuna wariya ba.
A gefe guda kuma, kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN ta mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmin Nijeriya a daidai lokacin da suke gudanar da bukukuwan karamar Sallah, yayin da a lokaci guda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki mummunan kisan gillar da aka yi wa mafarauta 16 a garin Uromi na jihar Edo.
A cikin sakon taya murna bayan kammala azumin watan Ramadan, shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya jaddada muhimmancin bikin Idin karamar Sallah a matsayin lokacin tunani, da yin addu’a ga al’umma.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a jiya ne Shugaba Tinubu ya gudanat da bikin Sallah na farko a Abuja tun shekarar 2023.
Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, Babban Mai Bai Wa Shugaban kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, da wakilan majalisar zartarwa ta tarayya, da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci Sallar.
A nasa bangaren, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya taya al’ummar Musulmi barka da sallah, inda ya bukace su da su yi addu’ar samun hadin kan al’umma.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Hon. Eseme Eyiboh, Akpabio ya jaddada muhimmancin hadin kai tare da karfafa gwiwar Musulmi da su ci gaba da hadin kan kasa.
Hakazalika, gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya taya al’ummar Musulmin jihar da ma kasar murnar bukukuwan karamar Sallah.
A sakonsa na fatan alheri, mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yinka Oyebode, a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin kwanaki 30 tare da jaddada bukatar ci gaba da gudanar da ayyukan ibada da ake nunawa a watan Ramadan duk shekara.
Gwamna Oyebanji ya hori al’ummar Musulmi da su rika amfani da koyarwar wata mai alfarma a duk wani aiki da za su gudanar, inda ya bukace su da mabiya sauran addinai su ci gaba da zama cikin soyayya da zaman lafiya da juna a matsayin ‘yan’uwa.
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira ga al’ummar jihar da su amfani da darasin da suka koya a cikin watan Azumin Ramadan, sannan su rungumi zaman lafiya da hadin kai.
Gwamnan, a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata jim kadan bayan Sallar Idin, ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallah, a karshen Azumin watan Ramadan.
Ya bukaci al’ummar Musulmin Jihar Zamfara da sauran kasashen duniya da su yi zurfafa tunani kan sadaukar da kai ga Allah kamar yadda aka yi a cikin watan Ramadan.
Hakazalika, gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya bukaci al’ummar Musulmi da su kiyaye dabi’u na hakuri, tausayi, hadin kai da aka koyar a cikin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature, ya fitar, ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, tare da karfafa gwiwar ‘yan kasa da su tallafa wa marasa galihu da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’ummarsu.
PDP, Atiku da Obi sun bukaci ‘yan Nijeriya da shugabanni su ji tsoron Allah da tausayi a tsakaninsu
Jam’iyyar PDP, Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma, sun kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kwatanta irin darusan da suka koya, kyawawaan dabi’un soyayya, hadin kai, zaman lafiya, hakuri, kamewa da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki da sauran kyawawan dabi’u da suka shafi gudanar da mu’amalarsu ta yau da kullum.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Hon Debo Ologungaba ya fitar, PDP ta bukaci ‘yan Nijeriya musamman masu rike da madafun iko a dukkan matakai da su sake sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu na nuna son jama’a bisa kyakkawan jagoranci, gaskiya, da rashin nuna wariya a dukkan ayyukansu tare da kawar da ayyukan cin hanci da rashawa, girman kai, magudi, da kaucewa nuna rashin sanin halin da al’umma ke ciki.
Mai magana da yawun babbar jam’iyyar adawar ya ce jam’iyyar ta damu matuka da yadda ‘yan kasar ke gudanar da bukukuwan Sallar Idi cikin hali na damuwa saboda wahalhalun da ba za a iya jure su ba na rashin kyawun mulkin jam’iyyar APC, wanda ya kara dagula al’amura a kasar cikin shekaru biyu da suka wuce.
Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a shekarar 2023, Mista Peter Obi, ya mika sakon fatan alheri ga Musulman Nijeriya, inda ya bukace su da su zama mdabbaka irin darusan da suka koya a Ramadan shi zai jagoranci rayuwarsu ta yau da kullum.
Mai magana da yawun Peter Obi, Mista Ibrahim Umar, ne ya mika sakon fatan alherin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Obi a cikin sakon nasa ya ce, “Addu’armu itace Allah Madaukakin Sarki Ya karbi addu’o’inmu da azuminmu a yanzu da kuma ko da yaushe.
“Hakika abin farin ciki ne a gare ni in yi buda-bakin Azumin watan Ramadan tare da al’ummar Musulmi daban-daban a fadin kasar nan, samun albarkarmu da jin dadin junanmu ba wai kawai watan Ramadan kadai ba, har ma ya zama wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum.”
Ya yi addu’ar Allah ya sanya albarka a darusan da aka koya a watan Ramadan, wanda yin hakan shi zai sanya “soyayya a zukatanmu, zaman lafiya da hadin kai za su bunkasa a cikin al’ummarmu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp