Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya soki ayyana dokar ta-baci da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas, inda ya bayyana hakan a matsayin wata manufa ta siyasa da nufin tsoratar da gwamnonin da ba za su goyi bayan tazarcensa ba a 2027.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa an dade ana fama da rikicin siyasa da barnatar da albarkatun man fetur a matsayin muhimman dalilai. Matakin ya kai ga dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida. A madadinsu, Tinubu ya nada Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da jihar.
- Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027
- Gwamnatin Edo Za Ta Binciki Kisan Matafiya ‘Yan Arewa A Jihar
Sai dai matakin ya haifar da adawa mai tsanani, inda kungiyoyin farar hula da kuma kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) suka yi Allah wadai da lamarin, wanda suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.
Har ila yau, Amaechi, a wata hira da DW Africa, ya zargi Shugaba Tinubu da yin amfani da dokar ta-baci a matsayin makamin rufe bakin gwamnonin ‘yan adawa da kuma kara karfafa mulki.
“Lamarin dokar ta-baci ya kasance ne tsakanin shugaban kasa da ministan babban birnin tarayya. Shugaban kasa na son a ci gaba da darewa a kan mulki. Suna so su tsoratar da gwamnonin da ba za su goyi bayansu ba a 2027. Don haka, ana yada jita-jita a ko’ina cewa idan ba ku yi hankali ba, shugaban kasa zai tsige ku,” in ji Amaechi.
Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka.
“Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa. Ba za su iya ba, saboda shi shugaban kasa ne da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, babu wanda zai iya sanya masa dokar ta-baci, saboda akwai rashin tsaro mai tsanani a arewa maso gabas, arewa maso yamma, hatta a kudu maso gabas da kudu maso yamma, amma ba a saka dokar ta-baci ba sai a Jihar Ribas.”
Amaechi ya jaddada cewa alhakin tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, ba gwamnonin jihohi ba, wanda hakan ya sa dakatarwar Fubara ba ta dace ba.
“Gwamnan Ribas ba shi da alhakin tsaro, ya rataya a wuyan shugaban kasa, to me zai sa a hukunta mutumin da bai aikata wani laifi ba?” Ya tambaya.
Tsohon gwamnan na Ribas ya zargi Tinubu da saba ka’idojin tsarin mulki na yadda za a cire gwamna daga mukaminsa.
“Shugaban ya yanke hukunci ne ta wajen kundin tsarin mulki. Sashe na 188 ya bayyana yadda gwamna zai bar mulki, ko dai ya mutu, ko murabus, ko kuma a tsige shi. Amma bai ce wata rana ka farka ba, wani mutum da ake kira shugaban Nijeriya zai fid da ka daga mulki, wanda hakan ya saba wa dimokuradiyyar Nijeriya.”
Amaechi ya yi kira ga mazauna Ribas da su bijire wa dokar ta-baci, sannan ya bukace su da su yi zanga-zangar lumana wanda dimokuradiyya ta amince da shi.
Da yake magana kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Fubara, Amaechi ya yi zargin cewa rikicin kudi ne kawai.
“Abun da ke faruwa a tsakanin Gwamnan Jihar Ribas na yanzu da Ministan Babban Birnin Tarayya, shi ne batun raba kudi, idan ba haka ba, mene ne na rigima? ‘Yan Nijeriya ba sa son cin hanci da rashawa a wannan lokaci, ban ga wani a kan titi yana tambayar ko mene ne matsalar ba, ko su biyun za su iya magana da jama’a su fada mana matsalar?”
Amaechi ya koka da yadda a yanzu Jihar Ribas na karkashin mulkin soja ne, inda ta hana ‘yan kasar cin ribar dimokuradiyya.
“Yanzu an hana mu cin gajiyar dimokuradiyya. Jihar Ribas ce kadai jihar da ba ta jin dadin dimokuradiyya a halin yanzu, sun kakaba mana mulkin soja da karfin tsiya,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp